Monday, 20 June 2016

MATAR MUTUM 101_105

[5/5,4:00.PM]BY FATIMA

MATAR MUTUM
101_105

NA
MRS UMAR


Innah na tsye a zaure tana ta faman dariya, sai ga baba lami tazo,da sauri ta karaso tace."toh mairo yau da alama duniyar tayi maki dad'i irin wannan dariya haka , toh yau kuma me kika aikata? "Hummm ke'dai bari yar uwa ai yau ina ciki'n farin ciki, wai yanzu wannan d'an iskan yaro yazo wai Ebba ba lafiya, ya kaita asibiti an bata gado shine yazo yafad'a wai naje,hummm yar uwa bama wannan ba ,ke bakya tunani kodai , ciki yad'erka ma shgeyar shine yazo yana so ya aure ta kafin asirisu yatonu, kinsan yaran masu kudi.

" lami ta ke'ce da dariya tace. "nima, fa yar uwa na dad'e ina zargin haka kai amma indai da gaski ne haka ,toh gaskiya da duniya tayi mana dad'i,kinga daga nan da ya mutum shkenn Muhabbat bata ba zaman Katsina don Wallahi nasan malam ba zai barta ta zauna mai gida bah shkenn kinga gida ya zama naki.
" Haka ne fa lami, kai Wallahi shiyasa nake sonki a duniya, Lami duk abinda zanyi tare mukeyi,toh wai ni Lami ya magana BOKA kuwa? "Hummm kwantar da hankalinki yar uwa kamar kinyi bak'o yamutu ai na koma wajen boka. yace " kar'kiji komai indai aljanu na duniyar nan toh Hameed ba zai tab'a auren Muhabbat ba,har abada."Innah tayi dariya tayi ihu tace. "Ihooo wayyo sai ni mairo Wallahi wazaija dani ,ya kwana k'iyama,ai Lami wallahi naji a jikina wannan shgen yaro ba zaikai labari bah saboda a duniya na tsani Muhabbat kamar yanda na tsani uwarta, au Lami mubar wannan magana tunda kinzo yanzu sai muje asibitin tare,muga ya shgeyar take. "Dukkansu suka ke'ce da dariya suka shga cikin gida Innah tana zuwa zane kawai ta sake Lami ta kalleta tace. " A'a mairo ai lokacin sallah yayi bazakiyi sallah ba kafin mutafi. "Innah ta wurga ma Lami harara tace. " au kin manta abinda boka ya gaya man ,yace na tsyar da sallah indai inaso aiki nan yayi kyau, koh don haka ai ni natsyar da sallah, dama can bata dameni ba, bakoda yaushe nake yibah yanzu kuma na samu sauki ai kawai mutafi.

"Kai jama'a wannan wace irin rayuwace Innah keyi kamar ba musulma ba, toh Allah dai yasa mudace Amin!!!
Bayan sun fito bakin titi suka nufa, suka hau mashin, suna zuwa suka samu Abba da Hameed zaune a dakin, Innah taje masu a ciki'n fuskar tausayi,har yanzu Muhabbat bata farkaba, bayan zuwansu ,suka gaisa Abba yadube Innah yace. " toh mairo ni zan koma gida, amma nan zaki kwana ko zaki koma gida sai da safe kindawo. " Innah tace, "a'a malam ai gara na koma gida saboda ba'abar gida bakowaba, kuma ai naga nan asibitin kudi ce ana kulla da ita ba abinda zai samita.
"Gaskiya ne mairo toh mutafi gida bawan Allah kai ma ya kamata kakoma gidan haka tunda ana kulla da ita. "Hameed yayi shru yana kallon Abba dake magana saboda abin mamaki yake bashi yanda Abba ke magana kamar ba namiji ba .Gaskiya Innah ta gama da Abba, ahankali Hameed sake kallon Abba cikin yar k'aramar murya yace. " toh Abba shkenn kugaida gida nima yanzu zan tafi amma ina jiran Dr ne yazo. "Toh sukace Dukkansu da Innah da Lami suka ce" toh shkenn Allah yabata lafiya sai gobe zamu dawo ,basu tsya sunji me zaice bah suka k'ara gaba,bayan fitarsu Hameed kujerar da yake zaune yajawota kusa da Muhabbat, Allah sarki ido ya k'ora mata yana kallonta, baisan lokacin da hawaye ya fara fita daga idonsa ba na tausayin Muhabbat yace, Toh wai ni wannan hawayen da nake na tausayin Muhabbat ni koko na sone? kai ina na tausayine amma kuma ai Muhabbat takai macen da kowane namiji zai sota. " yana ciki'n wannan tunani Muhabbat ta fara magana. "Wayyo yaya Hameed Dan Allah kazo kace'ceni zai rabani da mutumcina. " Hameed da sauri ya tashi ya dagota jikinsa yace "Muhabbat calm down am here ba abinda zaiyi maki I promise u. "Ahankali Muhabbat ta fara bude idanuwanta tana budewa taga Hameed zaune kusa da ita sai kawai ta kara shigewa jikinsa.......



®EXTREME HAUSA WRITER'S

Na MRS UMAR

No comments:

Post a Comment