[4/23,5:30PM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
. 71_75
NA
MRS UMAR
Muhabbat tana cikin kuka,sai ga mahaifinta ya dawo daga kasuwa. Tunda ya hangota, yasan akwai abinda ya faru,da sauri yak'araso wajenta,
Yace " toh saba'ba yau kuma me kikayi mata? "Da sauri tamik'e tsayi.
saboda tasan da innah da abbanta duk tafiyarsu dayace sai dai ba'bbanci shi mahaifinta ne kuma duk abinda yakeyi bah acikin haiyacinsa bane, yace "toh munafika mushga cikin yaja hannuta suka shga. Tunda ga zaure yake kiran sunan Innah....
Kamar tana jira ta amsa, yace " mata fito me yafaru yau kuma ke da wannan Yar duniyar yar? "Innah ta yatsina fuska, tace " wai daga tayi bak'o sai tace wai bazataje bah. shine nake mata fad'a shine fa tafita tana fushi,tafi son duk wanda yazo. ya zagemu ace munk'i yimata aure,
"Muhabbat sakin baki tayi tana kallo Innah cikin ban mamaki, tace " toh yau kuma Innah ta chanza magana haka cikin kwanciyar hankali. hummm na tabbata Innah akwai abinda zata kulla," Muhabbat duk acikin zuciyarta take wannan maganar....
"Abba yajuya ya kalli Muhabbat, yace" au dama saboda wannan maganar kika zauna a waje. Saboda kija mata zagi wajen jama'a. Munafika mai bak'in hali, "Lami tafito daga dakin Innah, tace "haba malam ai zagin ya isa haka yariya ce fa. abita a sanu, "ko yanzu Muhabbat mamaki maganarsu ke bata,
"Abba ya kada kanshi. yashga daki, Innah tajuya ta kalli Muhabbat, tace "ai sai ki shga cikin koh, Muhabbat tace "toh,
Lami tace" wa Innah ni zan tafi gida, " Innah ta rako Lami har zauren gidan, "sannan Lami tace " toh kinji abinda na gaya maki. idan wannan dan iskan yadawo yana Neman. auren wannan ballagazar toh ki nuna kinfi kowa murna,saboda ko mutuwa yayi bah wanda zaice da sa hannunmu aciki, Innah tace amma Lami zan iya hakuri har ya kawu kudin auren wannan shgeya kuwa, "Lami tayi murmushi tace" ai hakuri zaki har mucinma gurinmu..
saboda bana so ya mutu a garin nan.za'a iya zarginmu, Innah tace "toh shkenn na hakura. kigaida gida.....
****************
Hameed gida ya nufa yana zuwa yayi sa'a. su dady na zaune a falo. gabansa sai dakan uku_uku yake. yana tunanin ko dady bazai aminci bah da ya aure Muhabbat...
Saboda idan har yaji ita yar talla ce. Ahankali Hameed ya zauna saman kujera.yagaishe da su sannan yadube dady,
yace "dad I what to speak to u about some thing very important, dady yace " ina jinka, Hameed yace "dama dady akan wata yariya ne da na samu zan aura, dady yace " kai my son am very happy. Yarinyar waye kuma waye mahaifinta? "Hameed yayi shru yana tunani, dady yace" kai nake jira Hameed,
Hameed yace "dad ita ba yar kowa bace.mahaifinta talaka ne yariyar zan aureta ne akan wani dalili mai kar'fi, dad "yace meye dalilin naka na auranta? "Hameed yayi ajiyar zuciya yace "wallahi abinda yasa zan aure Muhabbat.yarinyar tana cikin wahala kuma mahaifiyarta bata gidan. Dady tseya kuji dalilin da yasa zan aure Muhabbat!!!!!!!?
"Nan fa Hameed ya fad'a ma mahaifinsa ko wacece Muhabbat, "kafin dady ya fara magana mom ta fara, tace " ai wannan maganar banza ne karasa warda zaka aura sai Yar talla. Ina da sake,
Dady yace "dakata saratu ai MATAR MUTUM kabarinsa. idan Allah yace Muhabbat matar Hameed ce bah wanda ya isa ya hana duk duniyar nan!!!!!!
Please masu kirana akan cigaban MATAR MUTUM am very sorry insha Allah zan karasa....
EXTREME HAUSA WRITER
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment