[4/27,8:00PM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
76_80
NA
MRS UMAR
Mom tace toh shikenan Alhaji , Allah yasa hakashi ne mafi alkairi. Dady yace"yauwa ko kefa Allah yabasa sa'ar taimakon da kayi niya, so don haka yanzu in nafita office zanje nasamu mahaifin kamal sai muje a ayi maganar aure, so when are u going back to port Harcourt?
"Hameed yayi ajiyar zuciya sannan, yace "Dad am going back in the next 4 days,insha Allah sannan hutunmu yakare. "
Dady yace "ok toh Allah yakaimu yafin lokaci zamu tseyar da lokaci aurenku insha Allah...
Mom tace" toh yaushe zaka kawo man ita mugaisa? " Hameed Yayi murmushi yace " mom ai islamiyyarsu daya da Milan ai tasan Muhabbat. " Hameed yana fad'i sunan Muhabbat dai_dai lokaci da Milan zata shgo falo da gudu ta k'araso ta fada jikin Hameed.
Tace "laaa yaya Ashe kasan Muhabbat shyasa ina gaya maka sunanta sai da kazabura yaya kenn. " Hameed ya daure fuska. yace "ke bansan shermen banza go and get ready to islamiyya, zan kaiki yanzu. " hummmmm yaya kace kanaso kaga Muhabbat dai.
"Hameed ya wurga mata harara. Mom tace "a'a dakata ai gaskiya ta fada. Hameed yace " ai mom keki'ke sakatar da wannan yarinyar.
"Dukkansu suka sa dariya har da dady, Milan ta tashi da gudu ta haura sama don sa kayan islamiyya,Hameed ma dakinsa yanufa Dan watsa ruwa, dady kuwa zama sukai shida mom suna shawara akan yanda Hameed har ya aminci da Muhabbat gaskiya sun godema Allah da yabasu da irin Hameed,
Suna cikin fira sai ga Hameed sun fito shida Milan yana rik'e da hannunta,dady yadube ta. Yace " toh sarki rigima har an fito? Toh Hameed in kaje ka gaida Muhabbat..
"Hameed yasosa k'eya yace ai dady bah wajenta zanje bah, zankai Milan ne kawai sai nadawo. Dady yace " ok toh sai kun dawo. "Dukkansu suka amsa da toh dady, sannan suka fito Hameed ya bud'e mota yashga Milan itama haka sannan yayi ma mai gadi hon yabud'e mai gate suka fita, suna tafiya a moto suna fira,
Sun kusan zuwa islamiyya kenan Hameed ya yanke wata hanya, Milan ta bud'e baki. Tace " yaya ina kuma zaka anan? "Hameed ya wurga mata harara yace "sa ido kiyi kallo, yana gama maganar dai_dai lokaci da Hameed yayi parking din motarsa k'ofar gidansu Muhabbat.
Minal tace " laaa yaya ina ne nan? "Hameed yace " fito kiga Ko ina ne. "Suna fitowa dai_dai lokacin da wani yaro zai wuce, Hameed yak'irasa. Yace "kai don Allah shga nan kace ana kiran Muhabbat...
" yaron yashga yasamu Innah zaune tana gyaran gyada, yayi sallama. Yace "wai wani mutumi yace" yana k'iran Muhabbat. "Innah tayi shru sai can kuma ta tuna wani abu sai tace "kace ga tanan xuwa , Innah ta dube Muhabbat..
Tace "Muhabbat bakiji ana k'iranki a waje bah, " hummmmm Muhabbat ai kasa magana tayi sai kawai ta sak'i baki tana kallon innah, don mamaki take yanda halin Innah yasauya say'i daya, cikin ranta kuwa cewa take ya Allah yasa halin Innah ya chanza, tana cikin tunani Innah ta sake yi mata magana ahankali ta tashi don fita taga waye,
Milan ta kalli yayanta, tace "au dama yaya kace gidansu Muhabbat zakazo? " Hameed ya wurga mata harara, yace "Milan kin cika surutu. " Toh yaya daga fad'ar gaskiya, "tana rufe baki sai ga Muhabbat tafito, tana fitowa Milan ta bud'e kofar mota tafito da gudu. Tace " Aunty Muhabbat kenn dama Ashe ke'ce matar da yaya zai aura baki gaya man bah? "Muhabbat tayi murmushi. tace " au shiya gaya maki ni zai aura? "Kafin Milan ta bata amsa Hameed yabata amsa. Yace "eh nina gaya mata, Dan haka yanzu jike shrin islamiyya zamu wuce da ke. " Muhabbat ta zaro idanuwa.. Tace "ai ni bah yanzu zanje bah sai anjima. " Hameed ya daure fuska yace "kishga kifito muna jiranki yanzu. " Muhabbat dataga Hameed ya daure fuska yasa ta wuce cikin gida don zuwa ta gaya ma Innah tana zuwa ta zamu Innah zaune inda tabarta, tana zuwa Innah ta daga kai ta kalleta, Muhabbat tsyi tayi ta kasa magana don dugun fadan Innah,
Innah kamar ta sani. Tace "lafiya kika tsya man a kai? " Muhabbat ta fara inda_inda. Tace "Innah dama.... " toh dama me? Muhabbat tace "Innah dama yaya Hameed ne yazo da kawarsa yace " wai in nashrya nazo su wuce dani islamiyya. "Innah tayi murmushi tace toh miye Muhabbat ai kutafi kawai, sai kindawo. " Muhabbat tace toh. " tafito abinta.
" ni kaina sai da nace gaskiya Innah ta sake hali Allah yasa da gaskene. Bayan ta fito ta nufi motar Hameed dama suna tsyi shida minal suna fira, Hameed yabud'e kofar mota yashga Milan zata shga gaba, Hameed yace "mai zakiyi haba don Allah malama koma baya ai yanzu matata zata shga gaban motata. " Milan tasake baki tana kallon yayanta, don taga say'i daya yayanta yasake hak'ida. Tace "ok . "ta koma baya abinta Muhabbat kuwa tsyawa tayi ta kasa shga sai da takai Hameed da yaga bata da niyar shiga yasa yafito ya bud'e mata kofar motar yakamata yasata a ciki, Milan ta ke'ce da dariya tace "wayyo yaya wannan irin Luv haka motarma bazata iya shga bah sai kasata wayyo ai in nakoma gida sai naba mom labari. "Hameed bai mata magana bah ya zagaya yashga mota, itako Muhabbat kunya duk ta kamata, sai da yashga sannan ya fizgu Muhabbat jikinsa ya rungumita minal ta zaro ido, Muhabbat tasake k'ara tace " nashga uku miye haka yaya? Ahankali yadagota ya kalle milan dake baya yace "Milan yanzu sai ki gaya ma mom da kyau na rungumi matata koh!!!!!!!
EXTREME HAUSA WRITER
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment