Thursday, 2 June 2016

MATAR MUTUM 86_90

[5/1,6:30PM]BY FATIMA

MATAR MUTUM
.
. 86_90.

NA
MRS UMAR


Kamal juyawa yayi yafito daga falon har!!!! yafito basu San ya shgo bah yana fitowa motarsa ya dauka yafita yana tafiya yana tunani yanzu ina zaiga Muhabbat gashi bai San gidansu bah,kan motarsa ya juya ya nufi inda suke zama ,kafin ya karasa wajen da suke zama yaga wata kamar Muhabbat,da sauri ya dana kan motarsa wajanta yana zuwa yaga itace kuwa ai kam yasha gabanta, Muhabbat tana murmushi ta daga kanta saboda tana tunanin ko Hameed ne ,Kamal ya bud'e mota yafito Muhabbat tana ganin Kamal ne ta daure fuska,Kamal ya k"araso gabanta.

Yace "malama Muhabbat dama kina duniyar nan." Muhabbat ta murguda mai baki, tace "bansaniba ina ruwanka dani,malam bani hanya na wuce." Kamal yayi murmushi. yace "Allah yabaki hakuri ni bada fad'a nazo bah before I want to tell u some thing dama Hameed ne ya aikoni yace nagaya maki bashi da lafiya sosai so dama yanzu gidanku zanje sai gashi Allah yasa na ganki." Muhabbat Tace "nashga uku me yasa meshi jiya fa muna tare dama kenn bashida lafiya? "Muhabbat bata San lokaci da hawaye ya fara fita daga idonta bah. " kamal yace "so yanzu zaki biyo ni muje ki ganshi koh? "Muhabbat ta share hawayen idonta. tace"A'a kabari zanje saboda yanzu ina talla amma idan na sayar zanje." Kamal yace" haba Muhabbat don't worry indai kayan tallarki ne karki damu, yanzu idan nakoma ban kai'ki bah Muhabbat ai bakiyi ma Hameed adalci ba."Muhabbat tayi shru tana tunani. "A gaskiya idan har banje naduba yaya Hameed ba ban kyauta bah saboda yaya SHINE GATANA." Muhabbat duk cikin zuciyarta take magana , ahankali ta daga kai ta kalle kamal. Tace "toh ba damuwa muje naganshi. " Kamal yayi murmushi mugunta... Yace "yauwa ko kefa." Muhabbat bata sake yimashi magana bah ta nufe motarsa ta bud'e baya ta shga,Kamal ma yazagaya yashga yasa key yatada, yana cikin driving ya kalle muhabbat ta cikin mirror . yace " this girl today am gonna teach u a lesson."Muhabbat tace na'am magana kake."kamal yace "no kawai ina tunani ne ." tace toh. "Kamal yayi murmushi yace "since u don't know how to speak English I have sold u.

"Ba inda kamal ya nufa da Muhabbat sai mai kud'i hotel,yana zuwa Muhabbat ta dunga zaro ido saboda bata tab'a zuwa irin wannan asibitin bah, bama asibitin bah ko unguwar bata saniba duk yayon tallarta kuwa,kamal yayi parking d'in motarsa yafito sannan Muhabbat ta fito. Yace "toh munzo Muhabbat mushga ciki." Suna zuwa kamal.yace "toh tsya nan na amshi kati kinsan irin wannan asibitin ba'a bari mutane na shga sai an basu kati saboda tsaro." Muhabbat bata ce komai ba Kamal yajuya yanufe wajan receptionist don biyan kud'in d'aki ahankali ya juyo ya kalleta yana tunani ko tana kallonsa kwatakwata hankalinta baya wajansa da sauri ya biya kud'i aka bashi key d'akin da yakama,sai da yaje ya bud'e d'akin kafin yadawo. Yace" mata muje yana sama."Muhabbat ta bishi a baya sai da sukaje dai_dai kofar sannan. Yace "shga." tana shga Kamal bita da sauri ya rufe kofa Muhabbat cak ta tsya saboda yanda taga alamar d'akin bah asibiti bane da sauri ta juyo zata fita ina kamal yarufe kofa ,Muhabbat sai ta d'aure.tace "ina yaya Hameed d'in yake? " kamal ya kece da dariya. Yace "au wai kina tunani Hameed na nan toh kinyi kuskurin biyo ni don wallahi yau sai kinyi da nasanin sani na a duniya Muhabbat.
" Muhabbat ta fashe da kuka. tace"don Allah karufa man asiri wallahi ni ba yar iska bace. "Muhabbat takai hannunta zata bud'e kofa, Kamal ya rik'e mata hannunta ya fincikota ya jifata kan gadon d'akin, Muhabbat ta fasa wani irin ihu mai kar'fi......



Toh makaranta da alama kenn Allah yaba Kamal sa'a ?

®EXTREME HAUSA WRITER'S


NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment