[4/30,2:30PM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
.
81_85
NA
MRS UMAR
Milan shiru tayi takasa magana ahankali Hameed yasake Muhabbat, akan yana sakenta kamar tana jira takai hannunta zata bud'e kofar, Hameed yayi saurin fuzgota takara fadawa jikinsa ya rufe kofar mota sannan ya tayar da motarsa Milan bata dadara bah .tace "wayyo duniya yau ina gani wani abu, yaya ai wannan soyayyar yan india kuke. " Hameed ya juyo ya wurga mata harara yace "Milan just keep quite or i will deal with u. " Milan tayi shru sai dariyar zuciya take da ta kalle Hameed ta cikin mirror suna hada ido sai ta sun kuyar da kai kasa ta keci da dariya, Muhabbat ko duk kunya ta kamata tarasa inda zata sa kanta saboda kunyar Milan, kanta tasa cikin cinyoyinta ta kasa d'ago kai, Hameed ya kalleta yayi murmushi ya girgiza kansa yaci gaba da driving d'insa , Milan ta sake kallon yayanta. Tace "which time will they put the date of ur marriage? " Hameed ya wurga mata harara. yace "I don't know Milan wlh kin cika surutu." Yana rufe baki dai_dai lokaci da motansu,, ta isa gate din islamiyya, yana tsyawa Muhabbat ta kai hannunta zata bud'e kofar mota Hameed ya rik'i hannunta . yace "ina zaki kike sauri? toh kitsya zamuyi magana dake yanzu." Muhabbat na so ta kwaci hannunta daga garesa amma takasa, taji rok'on maza ballatana soja, Muhabbat bata San lokaci da hawaye yadinga fita daga idonta bah . Milan tace "yaya please kabarta mutafi class.
" Hameed ya juyo ya wurga mata harara yace "ina ruwanki please just go, ki tafi yanzu zatazo, zamuyi magana da matata. " Milan ta yatsna fuska. Tace "yaya ai ba inda zani sai naji me zaka gaya mata. " cikin fushi Hameed ya daka mata tsawa. Yace " Milan ina wasa dake? "Milan ta turo baki ta bud'e mota tafita tana fushi, Muhabbat itama takai hannu zata bude kofar Hameed yasa key yarufe, tayi_tayi ta bud'e ta kasa haka ta hakura sai ta koma bashi hakuri idonta a kasa tana hawaye, ahankali Hameed ya juyo ya kalleta. Yace " please am sorry Muhabbat wallahi ba haka halina yake bah nayi haka ne don Milan ta tabbatar ina sonki but am sorry my sweet sister wallahi har yanzu ke kanwata ce , kuma maganar da zamuyi dama inaso nagaya maki nayi ma iyayena maganar aurenki sunce bah matsala sun aminci so d'an haka yanzu insha Allahu su Innah kawai suka rage kuma suma zamu tsya da addu'a ba za'a samu matsala bah. "Muhabbat ta daugo kai tana kallonsa har yanzu hawaye fita yake a idonta , Hameed ya ciro Hanki ya dago fuskarta yafara share mata hawayen idonta, Muhabbat bata san lokaci da ta k'ara fashewa da kuka bah, ta fada jikin Hameed...
Tace " wallahi yaya na tabbata indai Innah na raye toh wallahi bazata barni nayi aure bah tayi wannan alkawarin. " maganar da Muhabbat keyi yak'ara sawa ta bashi tausayi , ahankali ya dago hannunsa ya fara bubuga bayanta tamkar jaririya yana fad'in. " ya isa kukan haka Muhabbat ai duk abin Innah batafi k'arfin Allah bah, inaso ki sani idan Allah yace ni mijinki ne toh bah Wanda ya isa ya hana , shi yasa hausawa ke cewa MATAR MUTUM KABARINSA ,Muhabbat idan har Allah yace ni mijinki ne toh bah Wanda ya isa ya hana duk duniyar nan...
"Sannan ya dago ta daga jikinsa yafara share mata hawaye yana bata bakin har ta dai na kuka sannan yabud'e mata k'ofar mota, tafita abinta, tana zuwa ta samu Milan zaune Muhabbat tayi mamakin yanda ta ganta, saboda ba alamar fushi a fuskarta sai ma murmushi,haka ta karsa wajenta suna cikin fira har malam yashgo bayan sun gama karatu aka tashsu kowace ta kama hanyar gida, Milan tana zuwa gida ta samu Hameed zaune a falo shida mom suna fira tayi sallama sannan ta karasa ta zauna kusa da mom, ta daga ido ta kalle Hameed ta kece da dariya Hameed ya d'aure fuska Milan tana ganin haka ta tashi ta haura sama....
**************************
Dady bayan ya tashi office ,bah inda ya wuce sai gidan mahaifin Kamal don yasanar dashi Hameed ya samu mata kumasu tsyar da magana ranar da zasuje, dady yayi sa'a yasamu mahaifin Kamal yayi masa tarba sosai , bayan sungaisa.. dady yace " dama Alhaji akan maganar danka yakawoni saboda yasamu matar aure shyasa nace bari nazo na gaya maka sai muje ayi magana. "Alhaji yace " kai amma naji dadi yarinyar ina ce, kuma waye mahaifinta? "Dady yayi ajiyar zuciya sannan. Yace"Muhabbat ba Yar kowa bace asali ma ita Yar talla ce. " nan fa dady yayi ma mahaifin kamal bayani ko wacece Muhabbat, tunda mahaifin kamal yaji wacece Muhabbat ya tausaya mata sosai . yace "toh Allah yasanya alkairi...
Hummmmm tur k'ashi ashe duk maganar da su dady keyi a kunnan kamal yana tsye yana jinsu, kawai sai yajuya ya fita. yace" ai wlh Hameed in kasan wata toh baka San wata bah sai nasaka KAYI NADAMA wallahi......
Toh makaranta ko wane matak'i kamal zai dauka?
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment