Sunday, 15 May 2016

MATAR MUTUM 66_70

[4/21,2:30PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
. 66_70

NA
MRS UMAR

Bayan mai mashin ya sauke su Innah, ta hango Muhabbat tsaye ita da hameed. Da sauri ta k'araso wajen su.
Tace "" au yau ma ka biyo ta toh wallahi yau zanyi maganinka,
" Innah tacima Hameed kwalar riga Ta fashe da kuka, tace "yanzu duk abinda kuke bai isheka bah machuchi azalimi, " duk yan unguwar da sukaji maganar Innah saida suka fito amma da sunga ita da Muhabbat.. ne sai sunkoma gida..

Hameed ransa yab'aci sosai saboda a rayuwasa yana bak'in cikin cin fuska.ya daugo idonsa har sun chanza kalla sun kuma jajawur kamar wuta. Morah tasa ta motsa soja yayi fushi,

Hameed Yace "Innah wallahi kin ban mamaki. Ai ji nake yanzu bah mai irin halinki a duniya toh bari kiji. Idan'ma mutuwa zakiyi kiyi na dauki alkawari zan aure Muhabbat!!!
Kuma auren bazai dauki wani lokaci bah. Zan rabaki da ita saboda rashen imaninki yayi yauwa,
Innah tace " nashga uku yaro nike banda imani, " sai kuma can tayi murmushi takaici Wanda yafi kuka,
"Yaro baka San wuta bah sai ka taka. ai ni wutace kuma wallahi zanyi maganinka. zan b'atar dakai kamar yanda na kora uwarta a cikin garin nan, " Hameed yayi murmushi,
Yace "ai kar'ki manta ni da Allah na dugara bah da boka bah.ai duk abinki sai na aure Muhabbat... "ya juya ya kalle Muhabbat tana ta kuka, Yace " haba matata kukan me kike ki. share hawayenki I promise u. zan aure ki kuma no one can stop me from marying u, Innah tace "Munafiki ai zan ga yar'da za'ayi ka aureta indai ina rayi. Ba kai ba auren ebbah.shen wai kai d'an gidan uban wai a garin nan? " hameed yayi murmushi yace "ni d'an gidan mutunci ne Wanda suka San darajar dan adam, "nan fa Innah ta fara zagen hameed, " Lami tace "haba Mairo ya kina b'ata yawon baki'nki. " Lami taja Innah cikin gida,...

"Innah cewa take " Lami ki bar'ni da Dan iskan yaro. Yau sai na nuna masa rashn kunyarsa ta karya ne, "haba Mairo ai kar'ki manta komai yazo karshe. wallahi aikin bokan nan nayi.kuma tunda munga abinsa iskanci ne toh ni zan koma wajen boka.kawai a rabasa da duniyar gaba daya, " Innah tace "yauwa Yar uwa!!!!
Ai idan har BOKA yayi man haka toh ya gamaman komai a duniya....
Zan'so naga wannan d'an iskan baya duniya, Lami tace "ai karki damu. Ai Muhabbat ita da jin dad'in rayuwa har abada sai dai taga wasu nayi amma bah ita bah..

Kai Lami shyasa nake sonki, " Lami tayi dariya tace "yauwa tsaya kiga na k'ora maki shi..

"Lami ta fito tasamu Hameed tsayi yana ta kallon Muhabbat. Ta k'araso wajansa, tace "bawan Allah don Allah kayi hakuri, " hameed ya juya ya kalleta saboda mamaki ma. ta basa ai duk abinda Innah ke k'ullawa ai tare sukeyi abinsu, amma sai ya nuna mata kamar bai San ma tanayi bah, Lami ta kara cewa "malam magana nake ma, " Hameed ya yatsina fuska yace " au wai dani kike? Lami tace eh, Hameed yace " toh naji malma zaki iya tafiya, "Allah sarki Lami takoma da Yar kunyar'ta, Muhabbat ta sulale kasa tana kuka, hameed ya durk'usa kasan, yace " haba Muhabbat kukan me kike wallahi alkawarin da nadaukar maki ba Wanda ya isa ya hanani aurenki....
Saboda iyayena basu da matsala yau zanje na samu dady d'ina, zanzo yasamu abbanki ayi maganar aure. Saboda naga bah abin da zai kawo karshen abin nan sai illa na aureki!!!!!!

Muhabbat tace "don Allah ka rufa man asiri ka barni. Ni dai wallahi bana sonka, "Hameed ya Mik'e tsayi, yace"mata toh nidai na gama magana ko ki soni ko karki soni nidai na gama magana....

Kawai yashga motarsa ya barta nan tana kuka..............


MXTREME HAUSA WRITER

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment