Friday, 14 April 2017

MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA 1

    *MAZA DA MULKI*
★★.       *MATA DA*    ★★
  ★.        *TAK'AMA*      ★



*بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم*

           *TSOKACI*

_wannan labarin k'irk'irre ne ba gaskiya bane nayi shine dan nishad'i da fad'akarwa, idan yazo iri d'aya da naka toh akasin haka aka samu.._


              *GARGAD'I*

 _Ban yarda wani ko wata su juya min labarina ta kowace hanya ba in ba tare da sanina ba ko ince izinina ba, koda kuwa sunan jaruman da ke cikin ne, duk Wanda yayi min haka toh Allah ya isa, dan haka a kiyaye._


```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION```
___________________________________

    *Story and written by*
           *_MRS UMAR_*

             *edited by*
      *_PRINCESS AMRAH_*

           *in dedication to*
        *_FIDDAUSI SODANGI_*

                 ```Page 1```

           *GARIN KATSINA*


~~Garin Katsina gari ne da ya tara d'umbin abubuwan ban sha'awa, Allah ya albarka cu garin Katsina da manyan masu kud'i,
 inda aka tara manyan 'yan boko, 'yan siyasa, harma da 'yan kasuwa,
uwa uba babbar Masarautarsu da ake ji da ita a duk fad'in Africa babu wanda baisan da zaman wannan masarautar ba.

   Ni dai ido kawai nake zarewa saboda yanayin garin ya bani sha'awa sosai, da yake ya kasance yanayin sanyi ne duk Wanda kagani zaka ganshi sanye da rigar sanyi a jikinshi,
ina cikin tafiya Allah ya sada ni da wata k'ofa kai na d'aga ina d'aga kai naga an rubuta ( *K'OFAR SORO*) a jikin k'ofar, harda tuntub'e naci saboda yanayin yanda akayi rubutunma kanshi abun sha'awane, anyishi da kalar golden hakan yasa ya haskaka wurin tamkar da zinari akayishi.
     Kai tsaye na danna kai cikin k'ifar duk da bansan inda zan nufa ba.
    A hankali nake tafiya yayin da naci karo da wani katafaren gida,
dakaga gidan kasan gidan sarauta ne, gidan yasha ado anyi mashi  Penti da red and white, ido na k'ara zarewa, juyowar da zanyi kenan na hango wata kyakkyawar yarinya na tafiya cikin k'asaita yayin da wasu 'yan mata na take mata baya su biyu, yanayin yanda take tafiya sai ka d'auka itace sarkin ko kuma sarauniya,
tafiya take d'aya bayan d'aya, tana jefa k'afarta kamar bata son taka k'asa, duka_duka shekarunta bazasu wuce shekara 17 ba, amma yanayin isarta da tak'ama sai ka d'auka irin babbar macen nan ce, sanye take da Gown har tana jan  k'asa, jikin rigar  red colour ne anyi mashi aiki da Golden, duk da rigar jikinta ta sauka har k'asa bai hana naga heel Shoes d'in da take sanye dashi ba, dogo ne kalar aikin rigar ta watau golden colour,
wani d'an siririn mayafi ta yafa a kanta tayi parking d'in gashinta, ta d'an ja mayafin baya ne shi yanuna gashin kanta wato (see me kamar yanda 'yan mata suke kiranshi),  fara ce  tana da tsayi bata da jiki wato siririya, sannan tana da dukiyar fulani daidai gwargwado, hancinta dogone kamar biro ko kuma ince margin biro d'in,
bakinta d'an k'arami ne kai kace teaspoon ma vmbazai iya shiga cikinshi ba, eyes d'inta manya ne k'wayar idonta bak'a ce har wani ruwa ke kwanciya a ciki.

      Chewing gum ne a bakinta a hankali take taunarsa cike da izza da tak'ama, taunar chewing gum d'inda take shi ya bayyana dimples d'in dake kwance akan kumatunta both sides.

   Duk tauna d'aya sai ta lumshe idonta kamar mai jin barci,
kafin ta k'arasa fitowa da gudu wasu motoci suka danno zuwa inda suke,
kai tsaye wajenta motocin sukayi parking, motocine na idon cin duniya kowace jikin motar an rubuta      *GIMBIYA FIDO* akai, anyi numbering nasu d'aya bayan d'aya,
 gaba d'ayansu suka fito daga motocin kamar zasu fad'i suka zube a k'asa suna kwasar gaisuwa,

"Barka da kwana gimbiya 'yar sarki jikar sarki Allah ya d'aukaka masarautar *SODANGI,* insha Allahu sai kin gaji mahaifinki".

  Cikin isa ta wani saki murmushi ta kad'a k'wayar idonta, a hankali ta juya ta kalli Hindu da sauri Hindu tace
"Gimbiya ta amsa".

Hindu ce ta bud'e mata d'aya daga cikin motocin,
Genesis k'irar ( *2016*) ta shiga Mairo tayi saurin d'age mata rigarta, saida ta shiga suka rufe k'ofar kafin Mairo ta shiga d'ayar motar, ita kuma Hindu ta shiga inda gimbiya take watau gaba, a cikin wadda aka rubutama *FIDO 1*
 sannan matasan sukayiwa motocin key,


***
Hindu da mairo kuyangun gimbiya Fiddausi ne dukkansu bazasu wuce sa'anninta ba,

d'aya daga cikin phone d'inta yayi k'ara da sauri Hindu ta mik'a mata tana yatsina ta amsa tayi Picking,

"Hello Princess kina gida kuwa?" Wata murya tayi magana a cikin wayarta k'irar galaxy grand prime wadda har yanzu ba'ayi releasing nata ba, itama har company taje akayi mata ita,

 "No bana gida" ta bada amsa a gajarce.
     "Kinje inane?" Aka sake jefo mata tambaya,
    "Bana son yawan magana fa and You've already know that, finally, na fita yanzu zanje restaurant d'in *zamburush* ki samine a can". Ta mik'awa Hindu wayar sannan tayi hanging uo nata.

 
Hindu tayi murmushi tare girgiza kanta saboda a kullum tana mamakin girman kai irin na uwar d'akinta,
duk inda suka bi sai anyi maganarsu daga mai cewa tana burgeshi sai mai zaginta, dama haka duniyar take, idan wani ya k'ika to tabbas wani sai soka komai bak'i da munin halinka.

    Kai tsaye zamburush suka nufa duka matocin uku tare sukayi parking, gaba d'aya mutanen dake wajen saida suka juya kallon motocin savoda yanayin tsarinsu ya banbanta da sauran motoci, kuma duka sabbine akayi ordering nasu saisa babu wanda ya gane cewa motocin *GIMBIYA FIDO* ne sabida kowa yasanta, ansan yanayinta ankuma san mktocinta.

     Mairo ta fito da sauri ta bud'e mata k'ofa, biyu daga cikin mazan sukayi saurin shiga cikin restaurant d'in, shima red and gold kamar adon rigar dake jikinta
sai da ta d'auki tsawan 5 minutes kafin ta fara zuro k'afarta, heel shoes d'inta da Chain d'in da ke k'afarta suka haska fuskar mutanen dake wajen,
duk jama'ar dake wajen suka saki baki dan ganin wacece a cikin wad'annan motocin, gaba d'aya ta fito da gangar jikinta,
tana fitowa cikin yatsina ta mik'awa Hindu hannunta, da sauri Hindu ta d'aura mata glass a hannunta,
  Saida tasa glass d'in kafin Hindu da Mairo suka take mata baya.....



              *N.W.A*


          _BY FATEEN SOJA_

No comments:

Post a Comment