MAZA DA MULKI
★★. _MATA DA_ ★★
★. *TAKAMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
____________________________________
_story and written by_
*MRS UMAR*
_edited by_
*PRINCESS AMRAH*
_In Dedication to_
*FIDDAUSI SODANGI*
```page 7```
Maganarshi ta tsaya ne saboda buɗe idonshi da yayi gaba ɗaya, cak ya tsaya dan ganin bah gimbiya Feedoh bace a gabanshi, cikin rawar murya yake furta'
“Zee what are you doing?”.
“Why? It's me your baby ko ka manta dani ne?".
Kasa magana ya yi sai dai hannunshi da yasa ya dafe kanshi yayin da idanuwanshi ke rufe, shafashi ɗin da take ne yasa shi saurin tureta ya fito daga cikin swimming pool ɗin, direct wajen inda aka aje towel ya nufa, ya ɗauki ɗaya daga ciki yana goge jikinshi, sanye yake dagashi sai d'an guntun bossier duk wani abu dake jikinshi ana ganinsa, cikin salo na y'an duniya ta biyoshi tana mashi wani irin wasanni wanda har saida ya biye mata........
»»»««««««««*****»»»»»»
_After one week_
Mom ce zaune gaban mai martaba tana ta faman magiya ya taimaka yasa Fiddausi kafin ta koma China taje Yola ta d'anyi kwana biyu ta gaida kakanninta saboda rabanta da zuwa tun kafin ta tafi makaranta a China, tasan ba wanda zaisa Fiddausi taje Yola sai mai martaba kawai shiyasa take magiya yayi mata magana.
“Shikenan Bahijja zanyi mata magana ai bazan hanata zuwa wajen y'an uwanki bah, ai bani kaɗai na haifeta bah, dama faɗan da kikaji ina miki saboda kyararta da kike ne, but don't worry i will do anything for you, bari ta dawo sai ta wuce jibe”.
“Yauwa mai martaba nagode sai dai ina naiman alfarma?”.
“Tame?”.
“Dama mai martaba inaso idan zata tafi dan Allah kada a haɗata da kowa a barta su tafi daga ita sai Hindu”.
Mai martaba yayi ɗan jim kafin ya ɗan kaɗa kanshi yace'
“Toh shikenan idan haka kike so sai su tafi da Hindu idan yaso sai na kira aminina ya aiki direbanshi ya ɗaukesu ya kaisu ƙk'auyen, tayi kwana biyu.”
“Toh mai martaba Allah ya ƙk'ara maka lafiya nagode".
Mai martaba ya amsa da toh haka sukaci gaba da firarsu mai cike da so da k'auna.
*ZAMBURUSH*
Gimbiya Feedoh zaune take ita da Anum basu san wainar da mai martaba da mom ke toyawa bah, dukkansu fuskokinsu daɗe suke da glass sai wani shanƙk'amshi suke, yayinda Hindu da ta haɗa ido da gimbiya sai taji takaici a zuciyarta itako Mairo ko a jikinta, Anum tasa hannu kenan zata ɗauko wataƙkwalba a cikin jikarta muryarshi ta daki dodon kunnanta.
“Sannunku yan mata kunsan hausawa sunce masoyi baya fushi so am back again.”
Anum ce ta kwashe da dariya yayinda gimbiya ko inda yake bata kalla bah, ballantana tasan da mutum a wajen wayarta kawai take dannawa, cikin gadara Anum ta fara jifa mashi magana,
"Wow dogon gaye so you back again? baka gaji da gaya maka maganan da a ke ba kenan?".
"Stop am not talking to you".
Yana rufe baki cikin siga irinta y'an duniya kawai ya fad'i gaban gimbiya, abin mamaki duk jama'ar dake wajen sai da suka juyo kallonsu dan kuwa kowa abin mamaki ya bashi ace kamar Affan Khalil yana rok'on Mace ta soshi gaskiya ne gaba da gabanta aljani ya taka wuta,
Glass d'in dake idonta ta cire cikin murmushin mugunta ta k'ura mashi idon tana k'are mashi kallo,
idonta ta numshi tana tunanin muguntar da zatayi mashi,
"Please princess say something, I love u, wallahi idan baki soni ba zan iya mutuwa saboda ke please”.
Wasu hawaye ne suka fara bin fuskarshi wanda itama kanta sai da tayi mamaki, yayinda Anum ta saki baki tana kallonshi....
*N.W.A*
No comments:
Post a Comment