Friday, 14 April 2017

MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA 9

       *MAZA DA MULKI*
★★.       _MATA DA_      ★★
  ★.         *TAƘAMA*        ★




NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
__________________________________


         _story and written by_
                  *MRS OMAR*

          _in dedication to_
        *FIDDAUSI SODANGI*


              _page 9_


_Wannan page naku ne yan group ɗin Khalesat Haydar nagode da irin son da kuke nunawa novel ɗi na, Thank u  all_


     Muryarta na rawa ta furta'
 “Kai dogon gaye what are you doing in my house are you mad a...?”
  Maganarta ta tsaya ne sakamakon maganar Adda data daki dodon kunnenta.

 “Daughter keda wa kike ta faman faɗa haka? A'a Affan yau kaine a gidan namu sannu da zuwa.”
 Gimbiya Feedoh sakin baki tayi tana kallon Adda cikin zuciyarta take faɗin
  “Dama Adda tasan dogon gaye kenan ko yau ce ranar da ya fara zuwa wajenta no!! in yau ce ranar da ya fara zuwa wajenta ai bai kamata ta faɗi sunansa direct bah..
 “Fee! tunanin me kike haka inata magana.?”
 Da sauri ta dawo daga tunanin da take saboda maganar da Adda tayi mata da ƙk'arfi, cikin sanyin jiki ta zauna ɗaya daga cikin kujerun dake parlour, yayin da itama Adda ta zauna ɗaya daga cikin kujerar da ke fuskantar Affan tana murmushi ta kashe mashi ido ɗaya.
 “Adda dama kinsan wannan mutumin ne?”
 “Kinjiki Fee da wata magana ai Affan kamar ɗa yake a wajena, saboda ɗan ƙk'awata ne Hajiya Aisha yana yawan zuwa gidan nan gaisheni saboda yaron yana da hankali sosai, kin sanshi kenan?”.
 Da sauri gimbiya Feedoh ta kalleshi saboda duk maganar da Adda keyi idon Feedoh na kanta, shima ita yake kallo, cikin isa ta mik'e tana tafiya saida takai daidai ƙk'ofar shiga bedroom ɗin Adda tace'
 “Bansanshi bah just yaso yayi min kama da wani Stupid boy ne..”
 Ran dogon gaye ya ɓaci dan dai babu yanda zaya yi yasa yayi shiru, Adda ta kalleshi ta fashe da dariya tace'
 “Yanzu muka fara wasan.
 Sukayi dariya dukkansu, sun daɗe suna fira kafin yayi mata sallama ya fita ita kuma ta nufi ɗakinta wajen gimbiya Feedoh koda ta shiga ta sameta tana barci,
 dai_dai lokacin da zai fita yaci ƙkaro da Hindu abin ya bata mamaki da ta ganshi ya fito daga ɗakin Adda shiko suna haɗa ido ya watsa mata harara,
 cikin zuciyarta take faɗin “Anya gimbiya tasan dogon gaye yazo wajen Adda ko naje na gaya mata, no!! nasan in na gaya mata bazata yarda dani bah, saboda yanda gimbiya ke son Adda zata iya komai a kanta, toh ko Nom zan faɗawa, no idan na gayawa mom hankalinta zai tashi sannan zata gano inda ɗiyarta ke zuwa, saboda duk uwa ta gari baza taso ɗanta na zuwa zumburash bah, ballantana ɗiya mace, oh my God ya Allah karka ba Adda sa'a akan gimbiya Feedon Allah kodan halin mahaifiyarta masu kyau..

 Maganar  Hindu duk a zuciyarta take yinsu bata san lokacin da idanunta suka fara zubar da hawaye bah.....


  _After two days_

Gimbiya Feedoh a yau ji take kamar ta mutu dan haushi saboda duk hanyar da zata bi dan ta fasa tafiyar amma abin yaci tura, Mai Martaba yace dole sai taje har iya ta fada mawa watau mahaifiyar Mai Martaba, amma itama din sai bata bata goyan baya bah, shiyasa ta hakura zata tafi ba dan ranta yaso bah,....


   *ADAMAWA YOLA*

 Misalin ƙk'arfe 2:00pm dai_dai flight ɗinsu gimbiya ya sauka cikin airport ɗin dake cikin garin yola,
 suna isa dama already Dad yasa abokinsa ya turo dirvenshi ya daukesu ya wuce dasu k'auyen, bayan ya ƙkwashe kayansu yasa a mota sannan ya buɗe masu ƙk'ofar motar suka shiga ita dai Hindu babu ruwanta sai yanda akayi da ita,
 tafiya sukayi mai nisa kafin suka ɗauke hanyar wani kauye mai suna *WURO NYOMBE* kauye ne sosai saboda garin duk ramune da jar k'asa, haushi ne ya ƙk'ara kamata yanda motar ke zalle duk tabi ta gaji, birkin da driven ya taka ne yasasu suka tsorata ba kamar gimbiya, wani tsoho ne ke shirin ya ƙk'etare hanyar baima kula da mota bah saboda yasan ba koda yaushe mota ke bin hanyar bah,  shiyasa ya tafi zai ketare babu ruwanshi da duba hanya,
da sauri wani matashin yaro na kan Bicycle ɗinshi yayi sauri ya yarda keken ya nufi wajen tsohon, mai keken yaro ne matashi wanda shekarunshi bazasu wuce 23 bah, dogo ne fari tas yana da hanci idonshi sexy eyes ne sumar kanshi a ƙkwance take saidai an mashi irin askin nan na zamani mai suna punk bashi da kiba amma yana da fadin ƙkirji, kayan jikinshi kanana ne idan ka ganshi bazaka ɗauka ɗan kauye bane saboda ko a birni a talakkance irin kayan da zaisa kenan,
 cikin zafin rai ya nufi motar da sauri driven ya buɗe ƙkofa zai fito gimbiya ta hanashi.
 "Kai wane irin ɗan iskan driven ne da baka kallon gabanka yanzu da ka bigeshi me zaka ce..”
 "Dan Allah kayi hakuri wallahi ban kula dashi bane am....”
Cikin zafin rai gimbaya ta fara magana
 "Karma ya hakura mana dan Allah zo kaja mota mutafi."
 Maganar gimbiya ce ta daki dodon kunanshi cikin zafin rai ya ɓalli marfin ƙkofar da take zaune.
 "Au sai yanzu nagane ba ɗan iskan driven bane ashe kece 'yar iskar.
 "Kai!! kasan koni wacece da har kake zagina toh wallahi kajawa kanka da duk wani family ɗinka bala'i saboda ubana zai iya yin komai saboda ni.
 "Toh ina ruwana waye uban naki idan har kin isa inaso yau ɗin nan naga duk matanen dake kauyen nan kinsa an gama dasu."

 Wani matashi yaro ne wanda bazai wuce sa'arshi bah yazo yana bashi hakuri.
 "Haba Balatoni ai bai kamata kana faɗa da mace bah, ɗan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, tsaki taja ta buga ƙkofar motar yayinda driven yaja motar da sauri ita dai Hindu yunwar cikinta ma ta isheta......


         *N.W.A*

      Fateen......

No comments:

Post a Comment