MAZA DA MULKI*
★★. _MATA DA_ ★★
★. *TAƘAMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
__________________________________
_story and written by_
*MRS UMAR*
_in dedication to_
*FIDDAUSI SODANGI*
```page 8```
This page is urs my sweet *JEEDDH ALIYU* because you love me so much, yes thank you i will never forget you in my life, *FATIJIDDAH* i love u....
Cikin shu'umin murmushinta ta fara magana, duk magana ɗaya aiki ce a wajenta,
"Hmm! dogon gaye, you will never understand me, look at me, and look at you, zakaga da banbanci, so I'm warning you, stay away from me, this is my last Warning, aikin banza..”
Tana rufe baki tayi ball da table ɗin dake wajen wanda har sai da ya bigeshi ta juya ta harari su Hindu da sauri suka take mata baya, duk abin Anum kasa magana tayi sai binshi take da kallo, tanasa k'afa zata fita duk jama'ar dake wajen suka ɗauki ihu.
"Sai gimbiya!!! wow Allah yaja da ran masarautar SODANGI".
Murmushi ta saki mai cike da jin daɗi saboda a rayuwarta tanaso taga jama'a na bata girma, tana fita da gudu mutanenta suka buɗe mata mota tashiga da sauri, sannan sauran suka nufi tasu motar, tana cikin mota amma tana tunanin dogon gaye, ita kanta abin mamaki yake bata.
“Gaskiya ne the guy is handsome,
problem ɗinshi ɗaya, shi chocolate colour ne nikuma a tsarina nafi son farin namiji, uhumm..”
Ajiyar zuciya ta sauk'e mai ƙarfi wanda har saida Hindu ta juyo, saidai bata san abinda yasata sauke ajiyar zuciyar bah, saboda duk a cikin zuciyarta take wannan tunanin,
direct gida suka nufa da ita, yau anci sa'a saboda dogon gaye ta koma gida k'arfe 8:05pm, tana fitowa daga mota mutanen dake wajen suka dinga zubewa a ƙasa suna kwasar gaisuwa, kota kalli inda suke bare ta amsa, abin bai basu haushi bah, saboda in da sabo sun saba, kai tsaye ɗakinta ta nufa,
Tana dai dai shiga taci karo da ɗaya daga cikin ƙwarƙwarar Adda cikin ladabi ta duk'a tace
“Barka da zuwa gimbiya dama mai Martaba yace in ƙiraki yanaso yayi magana dake yanzu.”
Cikin isa ta juya, saida ta kusan isa ƙofar shiga bedroom ɗinta kafin tace
"Kice mashi ina zuwa”.
Bata tsaya komai bah ta tashi da sauri ta fita, itako mai mulki bata nufi ƙiran mai martaba bah, har saida ta gama abinda take, har wanka sai da tayi, cikin ƙasaita ta tura ƙofa,
zaune yake a parlour yayinda fuskarshi ke ɗauke da murmushin murnar yaga ƴartashi,
"Barka da dare.”
“Yauwa barka dai my daughter.”
“Dama mai Martaba naji Indo tace kana nemana ne.”
“Eh nina aika a kiraki, dama ba wata magana bace mai tsawo, inaso ki had'a kayanki jibi zaki wuce...”
Kafin ya k'arasa magana ta tareshi,
“Laah! mai martaba Dubai zan tafi ne? ”
“No zaki tafi Yola n....
“What? Mai martaba Yola kuma? gaskiya ni ba zanje kauye bah".
"what! are you mad? This is my decision i can not change my mind“.
Wani bakin ciki ne ya daki zuciyarta ji take kamar zata mutu dan haushi,
kamarta yanzu mai Martaba yace sai taje kauye ai wannan zubar da aji ne,
Maganar da Mai Martaba yasake yi ne yasa ta dawo daga tunanin da take.
“Toh zaki iya komawa ɗakinki zuwa gobe ki fara shirye shiryen hada kayanki dan jibi zaki wuce insha Allahu.”
A hankali ta tashi dan tasan tunda mai martaba ya furta haka toh bazai chanza bah,
duk maganar da mai Martaba keyi da gimbiya mom na tsaye tana jinsu, taji daɗi yau sosai yanda bai goyarwa ɗiyar tashi baya bah, dan haka ta turo ƙofar tasa tashigo ita kuma gimbiya, dai dai zata fita, abin mamaki kota kalli fuskar uwartata ballantana tace mata sannu, ita dai mom ko a jikinta saboda tasamu abinda take so,
shiyasa gimbiya ta fita jiki a sanyaye, ɗakin Adda ta nufa kai tsaye ko zuciyarta zatayi sanyi, bata tsaya komai bah ta tura ƙofar ɗakin, abinda tagani ne yasa ta tsaya cak,
muryarta na rawa ta furta.
“k.....
Toh makaranta wannan amsar taku ce, mai gimbiya ta gani ya bata mamaki a ɗakin Adda tsaya muga wa yafi ƙwaƙwalwa😀😀😀??????????
Taku ce dai
Fatin soja
Casinos & Slots | DMC
ReplyDeleteLooking for casinos with video 광주광역 출장안마 slots? Then you have come to 대구광역 출장안마 the right place. Play casino games 영주 출장마사지 with the best 오산 출장마사지 games available online from the comfort of 부산광역 출장안마 your home.