Friday, 14 April 2017

MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA 4

      MAZA DA MULKI'
★★.         _MATA DA_    ★★
  ★.          *TAK'AMA*      ★


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
_________________________________

        _story and written by_
                 *MRS UMAR*

                   _edited by_
         *PRINCESS AMRAH*

         _in dedication to_
        *FIDDAUSI SODANGI*



                     _page 4_




~~"Taya haka zata faru bayan kai kanka kasan halin princess yarinyar bata da kirki? yarinya ce da take jin kanta kamar itace sarkin ma, kai ko sarki baya nuna izzar da take nunawa".
  "Humm Haydar kenan, ina zato har yanzu baka san halina bah, humm! anshe goruba hannu kuturu ba wuya bane dan haka wait and see sai na dasa mata soyayyata a zuciyarta ko ta halin yaya ne wallahi kaji na rantse".
 "Toh ba zance maka a'a bah, amma kayi a hankali ni nasan halinta baki d'aya"
 "Hmm! inaso ka bincika min school d'in da take a China because..."

 "Kafin yak'arasa maganar ya cije lips d'inshi ya girgiza kai saboda shi kad'ai yasan mugutar da zai shuka mata, a wannan lokacin ne yayi parking a Guest house d'inshi inda ya tanada domin aje 'yan Matanshi,..

      °°°°°°°°°°°°°°

Wata kyakkyawar mace nagani zaune kan bed ta buga  uban tagumi sai tunani take, sanye take cikin kayan barci ta baza gashin kanta a baya da ka ganta kaga cikakkiyar bafulatana,
 duk bayan wani lokacin takan d'aga kanta ta duba agoggon dake manne a d'akin, k'ofar d'akin da aka banko ne yasata saurin d'aga kanta, tsawar da ta daka mata ne yasata tsayawa cak!

 "Dakata daga ina kike a wannan lokacin? yanzu Fiddausi a wannan lokacin zaki dinga dawowa gida? ki duba time kiga k'arfe nawa?"
 "Ido ta d'aga ta dubi agoggo taga k'arfe 11:05PM ta wane yatsina fuska ta nufi kan gado ta zauna, ko a jikinta.
 "Magana nake maki kika maidani 'yar iska tsaye tana magana"
 "Toh mommy me kike so nace maki? aidai kin san ba b'ata zanyi bah because ni ba yarinya bace, ko kina so na zauna a gida kina kallona ne?"

 "Shiru mahaifiyar tata tayi ta saki baki tana kallon d'iyarta saboda inda sabo ta saba da halinta, cikin sanyin murya ta zauna kan gado kusa da fido tace

 "Please Fiddausi listen to me, I'm ur Mother ba zanso duk wani abinda zai kawo matsala a rayuwarki bah, burina bai wuce kizama d'iya kamar sauran yara bah, a koda yaushe ina maki addu'a Allah ya kareki a duk inda kike, inaso kizama mai tsoron Allah saboda wannan ba rayuwa bace.."
   "Oh God! Mommy u will never understand me am telling u niba yarinya bace, dan haka ki barni nayi rayuwata yanda nake so".
 "Yanzu ni kike gayawa wannan maganar Fiddausi? ina guje maki ranar da zakiyi nadama ne"
 "Mtsss"

 Bata k'ara yima mahaifiyar tata magana bah, sai dai tsokin da ta buga ta finciki towel d'in dake kan mirror ta nufi toilet,
 Mommy kasa magana tayi sai dai hawaye dake bin fuskarta cikin sanyin jiki ta mik'e ta nufi k'ofar fita, a parlour gimbiya taci karo da Hindu tana tsaye tana sallah mommy ta girgiza kai saboda tasan gimbiya ta jata zuwa yawo shiyasa bata samu damar yin sallah bah, sai yanzu cikin shashek'ar kuka ta nufi d'akin mai  martaba,
Mai martaba SODANGI zaune yake kan sallaya yana lazimi k'ofar da aka turo ne yasashi saurin d'aga kanshi, yana ganinta ya gane akwai matsala,

 "Toh me yafaru kedawa kuma?"
 "Mai martaba kasan damuwata a kullum matsalata bata wuce akan Fiddausi ba, burina bai wuce ta zama d'iya kamar sauran yara bah, mai martaba kana sane da duk irin wulakanci da take shukawa mutane a cikin garin nan amma ka zuba ido kana kallon...."
 "Dakata...." mai martaba ya fad'i bayan ya d'agawa matarshi hannu cike da fushi yace....


 
        Aka TEEMA Lady

No comments:

Post a Comment