*MAZA DA MULKI*
★★. _MATA DA_ ★★
★. *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
______________________________
_story and written by_
*MRS UMAR*
_edited by_
*PRINCESS AMRAH*
_in dedication to_
*FIDDAUSI SODANGI*
_page 2
~~Suna shiga sukayi saurin goge mata kujerar da zata zauna akai, cikin yatsina ta iso wajen da sauri Hindu taja mata d'aya daga cikin kujeran ta zauna,
matasan nan su biyu suka fara jera mata kirari,
"Barka da isowa gimbiya Fido,
'yar sarki jikar sarki taka lafiya dai uwar d'akinmu, gaba sallamun baya sallamun taka lafiya dai gimbiya kinyi gaba babu gimbiyar da ta kaiki saidai ta k'asanki,
Mak'iyanki sun buga dake sun barki insha Allahu sai kin gaji mahaifinki".
Ta wani lumshi ido ta k'ara gyara zama saboda a rayuwata tanaso taji ana mata kirari sai kanta ya k'ara girma da fashewa, alama tayi masu da hannu ma'ana zasu iya tafiya waje, jikinsu na rawa suka kama hanyar fita Mairo da Hindu suka koma bayanta suka tsaya.
"Humm baabah kana ganin yarinyar nan yanda take isa sai kace itace sarkin?".
"Au! ai kad'an ma kagani yarinyar nan jinta take kamar itace sarkin, yarinya k'arama da shegen girman kan tsiya,
ko da yake mahaifinta ke da laifin yarinya k'arama ya fidda ta karatu zuwa k'asar waje".
"Kai baabah ina take karatun?"
"Naji ance wai a China take karatu".
"No wonder, dole ta zama haka saboda yana tunanin ita d'aya ya haifa saisa yake sangartata haka, yabi ya lalatata bata ganin kimar kowa a idonta".
"Dama hausawa sunce *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA,* kuma fa na gasgata hakan, wai abun mamaki sai mace ta dinga TAK'AMA kamar ita ke MULKIN saboda nan gaba yarinyar nan ta k'ara girma idonta ya kara bud'ewa toh wallahi talakawa zasuci ubansu wajenta sai kowa ya wahala".
Duk wannan maganar wasu samari ne ke yinta sunayi suna hangen Gimbiya Fido daga nesa.
Zamanta da kamar 10 minutes sai ga wata yarinya wadda itama bazata wuce sa'ar taba, sanye take cikin wasu english wears black Jeans da pink top, sunyi tight d'inta sai wani d'an siririn mayafi da ta yafa maganin babu, sai ga wasu mahaukatan hill shoes tasha, haka yasa duk mutanen dake wajen kallon gimbiya ya dawo wajenta, cikin isa da yatsina ta ida isa inda gimbiya take zaune, jikin table d'in dake wajen ta aje handbag d'inta cikin yatsina ta fara magana,
"Princess I don't know what is wrong with u, I called u several times but u kept rejecting it why?"
Sai da gimbiya ta murmusa kafin ta d'auki k'afarta ta d'aura kan table d'in da ke wajen, ta d'aura k'afa d'aya bisa d'aya cikin isa ta fara magana,
tana magana tana taunar chewing gum duk magana d'aya sai ta lumshe idonta sannan ta bada k'iriss da chewing gum d'in.
"Am sorry Anum, I din't want to see ur call thats why".
Anum tayi ajiyar zuciya da sauri Mairo ta ja mata d'aya daga cikin chair d'in dake wajen,
gimbiya ta dubeta tace
"Anum what do u want to eat?"
"Humm I like SHAWARMA yes shawarma chicken I want to eat it".
Tana rufe baki gimbiya fido ta kalli Hindu da sauri Hindu ta juya ta nufi wajen serving d'in abinci
"Kai ai wallahi sai nayiwa yarinyar can magana kaji yanda ta shiga zuciyata kuwa?
"Humm bazan hana kaba dan wallahi nasan girman kan yarinyar nan tana jifa kamar ita ke MULKIN garin nan". "Kai mutumin forget girman kanta kar ka manta fa duk wata mace bata min wuyar samu, komai cikar izzarta kuwa".
"Toh sai ka dawo ni kam ba dani ba, ina nan ina zuba idona dan ganin yanda zata kaya tsakanin kai da ita, dan nasan ba zakuyi rabuwar arzik'i ba",
"Naji nidai sai naje".
"Yana tashi ya nufa inda su gimbaya suke direct babu ko kwana kwana ko alamar shakka ya isa wurinsu....
*KUCI GABA DA KASANCEWA DA* 👇
_FATEEN SOJA_
No comments:
Post a Comment