Friday, 14 April 2017

MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA 5

       MAZA DA MULKI'
  ★★.       _MATA DA_     ★★
    ★.          *TAƘAMA*      ★



NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
______________________________

          _story and written by_
                 *MRS UMAR*

                    _edited by_
            *PRINCESS AMRAH*

             _in dedication to_
       *FIDDAUSI SODANGI*


                  _page 5_


   Mai martaba ranshi yayi matuk'ar ɓaci, cikin zafin zuciya ya ɗaga mata hannu tare da fad'in                                                          "please Bahijja keep quiet i don't want to hear anything from you, because how many times I told you don't said anything to my daughter again, hmmm Bahijja i don't know what is wrong with you, ke kullum kamar bake kika haifi yarinyarnan ba?, kin ɗaura mata karan tsana,  babba dake amma kin sakama yarinya ido, ko motsi tayi akan idonki"...
 Mamaki ya hanata bari ya ƙarasa, ta tari numfashinshi, "Amma mai martaba... "Dakata ban gama magana bah, shekarata nawa ina ne man haihuwa? ban samu bah sai yanzu, toh ki sani zan iya komai akan farin cikin ƴata, rashin son da kike nuna mata ko 'yar uwarki bata nuna mata shi ta d'auketa kamar ita ta haifeta,

  Mai martaba yana magana ne cikin faɗa yayinda ta kasa magana sai hawaye da ke bin fuskarta na takaici, cikin sanyin murya ta furta
  "Allah ya huci ran mai martaba kayi hak'uri, inaji a raina nafika son Fiddausi, a kullum ina  mata addu'ar zama ɗiya ta gari kamar kowa, sai dai kash mai martaba duk kana da labarin abinda take cikin garin nan ta matsawa talakawanka, da zarar ta fita jama'ar gari tsoronta suke haba mai martaba shikenan sai mu sa mata ido duniya ta zagemu?"...
 "ke duniya zata zaga ni kam ba mai zagina saboda banga abinda ƴata keyi bah, dan haka ki tashi ki koma ɗakinki kafin ki sani ciwon zuciya"..

 Cikin ban mamaki ta mik'e dukda abun ba sabo bane a wajenta ba,
 saboda a kullum indai zata kawowa mai martaba ƙarar Feedoh toh a ranar sai sunyi faɗa, ta rasa yadda zatayi dashi,
haka ta koma ɗakinta zuciyarta cike da bak'in ciki da k'unar zuciya.

  ***************

  Washe gari!

  Wata mata ce naga ta tura k'ofar ɗakin gimbiya Feedoh, bak'ace sannan tana da ɗan faɗin fuska, tanada jiki da alama itama matar gidance, kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Feedoh, kwance take kan bed ɗinta yayin da ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ga phone ɗinta rike a hannunta tana dannawa, tana ganin matar ta iso ta tashi cikin murna haɗe da murmushi, kasancewar gimbiya Feedoh ba dariya take yi bah, idan ko har tayi dariya toh ta muguntace,

 "Adda sannu da zuwa, shine bazaki bari inzo da kaina, na gaidaki ba? sai kinzo da kanki,
 "Haba dai ta hannun damana ai ke sarauniya ce zan iya miki komai dan ganin farin cikinki, saboda ni ban haihu da mahaifinki bah, amma inaji a jikina kamar nina haifeki zan iya miki komai a rayuwa.
 "Hmmm na sani Adda, but Adda i don't know what is happen to my mother because she hate me so much, bata son ganin farin cikina tafison a kullum in dinga sakarwa talakawa fuska su rainani dana fara abu zakiga ta fara min wa'azi.
 "Hmmm! My daughter don't worry am Here for you, ki daina damuwa kinsan kema dole Bahijja taso talakawa dan kuwa su suka haifeta kinga ko babu yanda za'ayi taki talaka, so dan haka shawarar da zan baki babu ruwanki da wa'azinta kici gaba da harkarki, dama y'an kuɗi na kawu maki nasan baki da kuɗi a hannunki, so ga dubu d'ari da hamsin (150k) nan ki riƙk'e kafin a kawo min kuɗi.
 "Wow! Adda thank you very much shiyasa nake ƙk'ara sonki, bari kiga in kira Anum tazo yanzu,

 Wayarta ta ɗauko ta danna numbar Anum,
 duk a binan Mum ɗinta na tsaye itada Hindu suna jinsu, hawaye ne ya fara bin fuskarta,
 "Shikenan haka zan dinga yima ɗiyata tarbiya wata na rusawa, tana lalata min tarbiyar ƴa?
 "Karki damu ranki ya daɗi akwai Allah",

Da sauri ta dago kai saboda tayi tunani a zuciyarta take maganar, hannunta Hindu ta kama suka nufi ɗakinta..........




               *N.W.A*




           _FATEEN SOJA CE_

No comments:

Post a Comment