Friday, 14 April 2017

MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA 3

       *MAZA DA MULKI
★★.      *MATA DA*    ★★
  ★.       *TAK'AMA*      ★





NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
________________________________

           _story and written by_
                 *MRS UMAR*

                   _edited by_
             *PRINCESS AMRAH*

               _in dedication to_
          *FIDDAUSI SODANGI*


                _page 3_



~~"Hi princess!  You are so much beautiful princess, humm am so very happy to see u a....."
     "Dan Allah dakata mallam ko ince d'an talakawa!, shin wai wama yabaka damar da zakazo kana cikawa gimbiya dodon kunne haka?"

  Cikin zafin rai ya dubi Mairo da tayi maganar yace

"How dare u da zaki kirani d'an talakawa kinsan waye ni kuwa? Humm ko dayake bai kamata ina b'ata lokacina ina magana da kuyanga haka bah, sai mutuncina ya zube a idon jama'a".

 Yana murmushi yaja d'ayar kujera ya zauna daga gimbiya Fido har Anum ba wadda ta kalleshi, haka yaci gaba da zuba, kamar kurnar da ba dad'i,

"Oh sorry I forgot to tell u my name,
so  my name is Affan Khalil, my friends also call me  dogon gaye..."

 Kafin ya k'arasa rufe baki Anum  ta kwashe da dariya har cup d'in da ke hannunta yana shirin fad'uwa da sauri ta ajeshi tana dariya,
 Gimbiya Fido ta gyara zamanta sannan ta d'auki glass cup d'in kusa da ita ta kurb'i d'an Juice d'in dake ciki kad'an sannan takai dubanta ga Afran tace

 "Mustapha Khalil Senator represented of Katsina, shine mahaifinka ko kana da wani uban wanda yafishi?,
 Ahmad Basheer SODANGI ba Wanda bai san da wannan masarautar bah,
 a duk fad'in Africa so Who is Mustapha Khalil in all Nigeria? I think he is....d
 "Stop it Fiddausi SODANGI!  Rashin kunyar taki har tabar kan talakawa ta dawo wajen iyayenmu no!! that's impossible, baki isaba wallahi kinyi kad'an, iyayena sunfi k'arfinki, na dad'e ina jin rashin kunya da rashin mutunci irin  naki, to ni zan maki maganinta wa..."
 Kafin ya rufe baki kawai ta watsa mashi juice d'in dake hannunta sai dai kawai yaji saukarshi a jikinshi haka yasa duk jama'a dake wajen suka juyo kallonsu,

 "Look at me dogon gaye kake ko wa? These gurls that you called kuyangu sunfi k'arfinka, sannan kuma sun fika daraja a wurina, dan haka close your so called mouth and leave this place before insa ayi k'asa k'asa da kai"

Cikin zafin rai idonshi yayi jajir yace

"SODANGI u made a Mistake, ni kike fad'awa wannan maganganun? Hmm! Amma fa ki sani kin tab'owa kanki, saboda ni ba'a tab'ani a zauna lafiya, dan haka na baki bashin wannan ranar dan ba zance na yafe miki ita ba"

  "See this man, see me se wahala ooo, duk wannan abin da tayi maka baisa ka saduda ba?"

 Anum ce yanzu tayi magana shi yasa ya juya ya wurga mata harara,
     Tsoki yayi sannan ya juya ya nufi wajen abokinshi yana zuwa yaja hannunshi suka bar wajen,

    Anum ce ta karkace ta rage murya sannan tace ma Gimbiya Fido

 "Gaskiya princess this dogon gaye is very handsome guy, bashida tsoro ko kad'an, ya burgeni sosai, haka nake son ganin namiji jarumi ba malalaci ba, duk yanda ake tsoronki a garin nan baisa ko kad'an shi yaji tsoron ba,  irin yanda yake magana ma abun sha'awa ne, kuma..."
 "Anum are you mad? what is wrong with? Ina tunanin kin manta ko ni wacece ko?"

  "No gimbiya ban manta ba" Anum ta bata amsa,

  "Just forget that stupid guy, na kula d'an rainin hankali ne, and also  I don't like Nigerian guys at all, banga abunda ya burgeki ba game da wannan d'an rainin sense d'in".

Anum ce ta k'ara kwashewa da dariya harda rik'e ciki

 "Princess  I don't know what is ur problem, ke ala dole bakya son 'yan Nigeria, bayan kuma all ur family suna Nigeria".

 Hararar da gimbiya ta wurgawa Anum ne yasata yin shiru ba shiri tayi maintaining.

****

Driving yake amma ji yake kamar zuciyarshi zata buga saboda tunda yake ba'a tab'a mashi irin wannan cin mutuncin ba, ko makamancinsa ba'a tab'a yi masa ba.

 "Please friend calm down mana, sai da na fad'a maka halin yarinyar nan na hanaka zuwa wurinta  nake kar kaje but you refused, ga irinta nan ai ta wulak'antaka a banza".
 "Hmm Haydar don't worry, ai ba bulus taci ba, kasan halina tun asali ni ba'a tab'a ni a zauna lafiya, na d'auki alwashin sai na mata wanda yafi wannan"



                *N.W.A*

         _BY FATEEN SOJA_

No comments:

Post a Comment