Sunday, 15 May 2016

MATAR MUTUM 66_70

[4/21,2:30PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
. 66_70

NA
MRS UMAR

Bayan mai mashin ya sauke su Innah, ta hango Muhabbat tsaye ita da hameed. Da sauri ta k'araso wajen su.
Tace "" au yau ma ka biyo ta toh wallahi yau zanyi maganinka,
" Innah tacima Hameed kwalar riga Ta fashe da kuka, tace "yanzu duk abinda kuke bai isheka bah machuchi azalimi, " duk yan unguwar da sukaji maganar Innah saida suka fito amma da sunga ita da Muhabbat.. ne sai sunkoma gida..

Hameed ransa yab'aci sosai saboda a rayuwasa yana bak'in cikin cin fuska.ya daugo idonsa har sun chanza kalla sun kuma jajawur kamar wuta. Morah tasa ta motsa soja yayi fushi,

Hameed Yace "Innah wallahi kin ban mamaki. Ai ji nake yanzu bah mai irin halinki a duniya toh bari kiji. Idan'ma mutuwa zakiyi kiyi na dauki alkawari zan aure Muhabbat!!!
Kuma auren bazai dauki wani lokaci bah. Zan rabaki da ita saboda rashen imaninki yayi yauwa,
Innah tace " nashga uku yaro nike banda imani, " sai kuma can tayi murmushi takaici Wanda yafi kuka,
"Yaro baka San wuta bah sai ka taka. ai ni wutace kuma wallahi zanyi maganinka. zan b'atar dakai kamar yanda na kora uwarta a cikin garin nan, " Hameed yayi murmushi,
Yace "ai kar'ki manta ni da Allah na dugara bah da boka bah.ai duk abinki sai na aure Muhabbat... "ya juya ya kalle Muhabbat tana ta kuka, Yace " haba matata kukan me kike ki. share hawayenki I promise u. zan aure ki kuma no one can stop me from marying u, Innah tace "Munafiki ai zan ga yar'da za'ayi ka aureta indai ina rayi. Ba kai ba auren ebbah.shen wai kai d'an gidan uban wai a garin nan? " hameed yayi murmushi yace "ni d'an gidan mutunci ne Wanda suka San darajar dan adam, "nan fa Innah ta fara zagen hameed, " Lami tace "haba Mairo ya kina b'ata yawon baki'nki. " Lami taja Innah cikin gida,...

"Innah cewa take " Lami ki bar'ni da Dan iskan yaro. Yau sai na nuna masa rashn kunyarsa ta karya ne, "haba Mairo ai kar'ki manta komai yazo karshe. wallahi aikin bokan nan nayi.kuma tunda munga abinsa iskanci ne toh ni zan koma wajen boka.kawai a rabasa da duniyar gaba daya, " Innah tace "yauwa Yar uwa!!!!
Ai idan har BOKA yayi man haka toh ya gamaman komai a duniya....
Zan'so naga wannan d'an iskan baya duniya, Lami tace "ai karki damu. Ai Muhabbat ita da jin dad'in rayuwa har abada sai dai taga wasu nayi amma bah ita bah..

Kai Lami shyasa nake sonki, " Lami tayi dariya tace "yauwa tsaya kiga na k'ora maki shi..

"Lami ta fito tasamu Hameed tsayi yana ta kallon Muhabbat. Ta k'araso wajansa, tace "bawan Allah don Allah kayi hakuri, " hameed ya juya ya kalleta saboda mamaki ma. ta basa ai duk abinda Innah ke k'ullawa ai tare sukeyi abinsu, amma sai ya nuna mata kamar bai San ma tanayi bah, Lami ta kara cewa "malam magana nake ma, " Hameed ya yatsina fuska yace " au wai dani kike? Lami tace eh, Hameed yace " toh naji malma zaki iya tafiya, "Allah sarki Lami takoma da Yar kunyar'ta, Muhabbat ta sulale kasa tana kuka, hameed ya durk'usa kasan, yace " haba Muhabbat kukan me kike wallahi alkawarin da nadaukar maki ba Wanda ya isa ya hanani aurenki....
Saboda iyayena basu da matsala yau zanje na samu dady d'ina, zanzo yasamu abbanki ayi maganar aure. Saboda naga bah abin da zai kawo karshen abin nan sai illa na aureki!!!!!!

Muhabbat tace "don Allah ka rufa man asiri ka barni. Ni dai wallahi bana sonka, "Hameed ya Mik'e tsayi, yace"mata toh nidai na gama magana ko ki soni ko karki soni nidai na gama magana....

Kawai yashga motarsa ya barta nan tana kuka..............


MXTREME HAUSA WRITER

NA MRS UMAR

MATAR MUTUM 61_65

[4/19,1:30PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
61_65

NA
B MRS UMAR

Ya'ya kasanta ne? "Hameed yayi murmushi, yace "no kawai naji kamar natab'a jin mai irin sunan ne, "kai!!! yaya ka fad'i gaskiya in'ma kasanta ne, toh bah matsala she is my friend I will make way for u, "ke ina wasa da'ke i don't even no the girl how can I marry her ? " hummmmm yaya don't worry nasan baka santa bah,
"OK amma me tace "meki da kika tambayita tana kuka, ? minal tace " A'a yaya ai kace baka son maganarta toh dan haka I will leave u,
Hameed yace "OK na barki tunda bazaki fad'a men bah. But yau ni zan kai'ki islamiyya, ""minal ta buga tsalle, tace ""yaya da gaske zaka kai ni Islamiyya? "Eh mana zan kai'ki.

""Kai amma naji dad'i , Idan mukaje zan nuna maka Muhabbat, Hameed yace "toh my sister yanzu inason in'fita sai nadawo, " toh yaya nima bari naje wajen mom a kitchen,,,

Bayan fitar Minal.....
daga dakin Hameed,
tashi yayi ya dauki makolin motarsa. Bah inda ya nufa sai gidansu Muhabbat, yana zuwa yasamu, yaro a k'ofar gida yaturasa Dan yak'ira mai Muhabbat,

Allah sarki, Muhabbat da sauri ta fito kasanciwar yau innah bata gida, tana fitowa ta ga hameed tsaye a jikin motarsa ,
Tayi mur'na da ganinsa sosai,
Muhabbat tace ""Yaya sanu da zuwa, hameed yace " yauwa my sister yakike? Muhabbat tace "lapia qlau, " hameed yadaga kyakkyawar fuskasa ya kalleta sosai, yace " nazo ni inaso muyi magana dake I have an Important issue to discuss with u , amma yau ina innah?naga kin fito da da sauri, "wallahi sun fita ita da babah Lami,

Hameed yace "ok muhabbat ina da k'anwa mai suna minal, tace "islamiyyarku daya, muhabbat tayi murmushi tace " eh wallahi jiya muka fara had'awa da ita,
Hameed yace "toh muhabbat inaso ki gaya man gaskiya me yasaki kuka jiya? Muhabbat ta zaro ido tace " ita ta tagaya maka ina kuka jiya?
"Hameed ya yatsina fuska yace " bah wannan na tambayiki bah, ina tambayarki ne a kan kukanki na jiya,
"Cikin murya kasa _kasa muhabbat tace " bakomai Allah ya'ya, "ok jindad'i ne yasaki kuka hummm muhabbat kenn yau na yanke shawara daga yau kukanki ya tsaya zan share maki hawayenki, muhabbat I want to marry u!!!!!!!

" Yana fad'in maganar dai_dai lokacin da su Innah suka, dawo daga wajen boka. mai mashen ya ajesu......


Tohhhh jama'a wai anyanka tatashi hameed yace "zai aure Muhabbat toh ko Allah zaisa, ya aureta.....


MXTREME HAUSA WRITER

NA MRS UMAR

MATAR MUTUM 56_60

[4/17,6:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
56_60

NA
MRS UMAR

Su innah babu inda suka yi tsinke,sai a wani kauye can cikin Niger .
Sunyi tafiyar k'afa mai nisa kafin suje wani kauye saboda tafiyar kasa ake sosai kafin aje garin, suna zuwa inna tayi sallama bokan yadaka mata tswa,yace "ke nan ba'ayi mana sallama.
Inna jiki na rawa lami tace tuba take boka,,

Yace "toh nasan abinda ke tafe daku,akan yarinyar kishiyarta ne, saboda bata so tayi aure toh bah damuwa shedanu sun San da zuwanku kuma anyi an gama, amma aikinmu akwai sharade idan muna aiki saiki tsayar da duk wani aikin lada, bake bah sallah sannan idan azumi yazo baza kiyi bah kin yarda?

Innah tajuya ta kalli lami,
Lami ta daga mata kai alamar ta aminci, ta dube boka tace "na yarda"
yayi dariya Wanda sai da duk wajen ya amsa yace "yauwa Yar gari"...

Yace "yanzu akwaiwata mastala kwaya daya. ,
"akwai wani shegen yaro..
ana fadan yaro sai da k'irjin inna yabuga," cikin ranta tace" kar dai ace wannan boka ma ba zai iya aikin bah wahalar banza zamuyi"..

Boka yace "ki kwantar da hankalinki, kina tunanin kamar bazan iya bah kamar wancan boka".

Innah ta zaro ido tana mai mamakin yanda akai har boka yagane abinda ke ranta, Lalli aikin boka nan zaiyi nasara,"
Boka yace mairo matsalarki ta warke tunda har kika zo nan "
"yaron nan idan yakoma wajen aikinsa toh shida garin Katsina har abada ita kuma bata ba aure.

Inna tayi dariya mugunta ita da lami kamar ansa uwarsu aljanna.
Boka yace "toh ga wannan laya ce kije ki sata a makabarta, "wannan kuma a cikin gida zaki rufe kinji koh? "Eh boka"
"Yauwa na Baku nan da sati biyu Ku dawo , " toh boka" mungode ,"hhhhhhhhhh" ai nan ba'ayi mana godiya saboda bama aikin Allah, toh boka ga wannan" ""ku'aje anan"

Suka aje nan fa suka fito suka kama hanyar gidan Nigeria...

(Wannan wace irin rayuwace irin tasu inna da lami sun manta Allah shine mai komai,
ya Allah kashiryar da bayinka Allah yasa mudace..)

Yau ta kama ranar Saturday hameed na dakinsa kwance idanuwansa a rufe yana mai tunani.
Ahankali Minal ta zauna dai-dai kafafunsa, tace "yaya what is wrong with u this days? Ahankali ya bude idonsa yayi murmushi yace
" no problem minal kawai ina tuna wani Abu ne, "kai yaya please tell me what is the problem" wallahi nasan akwai abinda ke damunka.

"humm minal sarkin rigima kenn Allah bakomai, toh shikenan yaya dama I want to tell u some thing ," humm ina jinki"
"yaya wallahi jiya da naje islamiyya nayi kawa yarinyar baruwanta,"

Hameed yace "But mai nagaya maki da zakije islamiyya, ba nace ba ruwanki da kawaye bah.

" toh yaya wallahi yarinyar naganta tanata kuka ne a class, shine taban tausayi har ta gaya man sunanta wai sunanta MUHABBAT,"
"Afirgice ya mike daga kwancen dayake"
what muhabbat!!!!!
cikeda alaman tambaya tace mai"Eh yaya, kasanta ne? ........

Makaranta akara hakuri da Mrs Umar....

EXTREME HAUSA WRITER

NA MRS UMAR

Thursday, 12 May 2016

MATAR MUTUM 51_55

[4/14,3:49PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM

51_55.

NA
MRS UMAR

Dan haka muhabbat ki kwantar da hankalinki"insha Allah komai yazo karshe" amma inaso na tambayiki kuma ki bani amsa, toh malam ina jinka,
Hummmmm muhabbat zaki iya aure na kuwa? Muhabbat ta zaro ido tace malam aure fah kace , eh kobazaki aureni bah? Aa malam ai kafi k'arfina ," Dan Allah karufa man asiri wallahi malam," kawai sai ta fashe da kuka, yace inajinki ki'ida maganarki mana, ina ta" kasa magana sai kuka..

Yace OK toh shkenn nasan abinda kike ma kuka bakya sona ne toh ba matsla tashi ki shga class,
ahankali ta dago tace aa wlh malam ba haka bane, hummmmm naji jeki zauna, cikin sanyi jiki ta tashi tashga ta zauna tunda ta zauna take tunani toh dama yau saboda maganar da malam umar zaiyi mata Allah yasa inna ta barta tazo islamiyya kenn..

Acikin zuciyarta kuwa cewa take gaskiya ina son malam Umar saboda na tambata idan na aure malam Umar nayi dacen miji sai dai kash in dai inna na duniyar nan baza ta " bar 'ni nayi aure bah" bata San lokaci da ta fashe da kuka bah,wata kyakkyawar yarinya ta dafata da alama Bakuwace a islamiyya tace haba Hauwa Allah me yafaru kike kuka? sai yanzu ta gane kuka take, tace bakomai , haba Yar uwa don Allah ki fada min mana, Allah bakomai, OK toh shkenn ni sunana minal Bakuwace ni a islamiyya nan Ke fah ? Humm sunana muhabbat wow sweet name, so kinga dama a islamiyyar nan bani da k'awa yanzu inaso muzama abokai kin yarda? Muhabbat ta daga mata kai alamar eh..

Suna cikin maganar sai ga malam mai hadisi yashgo nan suka tsya da maganarsu,
Bayan yagama masu aka tashsu, minal tace toh ni yanzu za'azo daukata kefa ina gidanku,humm gidanmu ba nisa sosai yanzu zan karasa, aa kitsya sai muwuce dake," aa wlh nagode , toh shkenn tunda bakya son na hakura, muhabbat tayi murmushi tace aa wlh bahaka bane ina dai sauri ne , haka sukayi bankwana ta dawo gida ..

Inna ce keta ruwan balai wai" Dan sunje wajen boka yace masu gaskiya aikin nan yafi k'arfinsa saboda duk sanda ya aiki shedanu aljanne dan suyi ma Hameed mugun abu sai sutarar yana addua sai dai su dawo,,
Inna tace dama a duniya akwai aikin da yagagari boka tsiga, lami tace haba Yar uwa kwantar da hankalinki kamar kinyi bako ya mutu ai na samomana mafita akwai wani boka a Niger bokan aikinsa kamar yankan wuka ne sha yanzu magani yanzu nima wata kawata taje wajansa sune take bani labari,
Haba lami dama kin San da wann boka baki gaya man bah.
Toh kiyi hakuri yanzu zamu Bari gobe da safe sai mutafi,
Kai Ai jinake kamar mutafi yanzu, aa mubari sai gobe dai, toh shkenn ....

Washe gari
Su inna suka kama hanyar Niger dan zuwa wajan boka....


Toh jama a ko in su inna sukaje wajen boka ko Allah zai basu sa a.....


NA MRS UMAR

Wednesday, 11 May 2016

MATAR MUTUM 46_50

[4/11,6:40.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
.
. 46_50.

NA
MRS UMAR

Humm muhabbat am sorry I am familiar with English sai kiyi hakuri dani, yauwa abinda nake so dake muhabbat ki" k'ara hakuri insha Allah zan taimakeki , muhabbat ta zaro idanuwanta a waje , hameed yayi murmushi Wanda sai da yabaiyana kyakkyawar fuskasa yace ki kwantar da hankalinki nasan abinda kike tsoro kada inna tayi man wani Abu toh insha Allah ba abinda zai faru dani sai alkairi kinji koh? Ki dauke ni a matsyin yayanki uwa daya uba daya daga yau hawayenki zasu tsya insha Allah, toh Yaya nagode amma ina tsoron Allah ina tsoron inna saboda bata da imani a ranta ko alama ,,humm karki damu ai duk abinta batafi k'arfin Allah bah yauwa yanzu kin"rik'e sunan garin da mamanki take a Cameron? Aa wlh dama kakata tasani kuma Allah yayi mata rasuwa, kawai sai ta sake fashwa da kuka,..
ahankali yadaga kanta yana share mata hawayen idonta please muhabbat stop crying I promise u zan taimakeki kota wane hali inda bai sa6ama shari'a bah kinji koh ? Tace toh , yauwa kanwata toh yanzu mutafi na kaiki gida ko? Aa zan tafi talla yanzu, humm muhabbat don't worry zan saye kayan tallar kinji mutafi yakama mata hannu , ahankali ta kallesa tace humm yayana mamana tace man ba kyau namiji ya ta6a matar da bah tasabah ,, humm muhabbat kenn kin manta yanzu ni yayanki ne ai yaya yakan kama hannun kanwarsa so Dan haka karki damu ba abinda zanyi maki my sweet sister yabude mata kofar mota tashga shima yashga ...

Sai da hameed ya kusan zuwa unguwarsu sann ya tsya da motarsa yace muhabbat zan barki anan because banaso naja maki duka, toh Yaya nagode , toh ga kudinki sai ki juye man kayan a mota saboda nasan in kika koma dasu gida in anjima sai kin fito talla, haka ne fa, yauwa my sweet sister kin gano kenn , " sukayi bankwana ta kama hanyar gida......

Kamal ne" zaune inda suka barsa yana magana a zuciyarsa yace hummm hameed kenn ai wallahi in kasan wata toh wallahi bakasan wata bah idanma son muhabbat kake toh wallahi kamakaro saboda narigaka sai na biya bukatata kafin inma aurenta zakayi sai kayi i swear to my God no one can stop me from what I want to do...
Yana cikin maganar a zuciyarsa sai ga hameed ya dawo yace ya abokina kamal wani irin kallo yayi masa ," humm dama in"dai irin wann kallo ne toh kamal gidan yazo , hameed ya yatsna fuska yace that is ur problem, kawai yashge motarsa....

Muhabbat tana komawa gida tasamu har baba lami tatafi gida tayi murna a zuciyarta saboda ta" San in har lami na gidan toh tashi ga uku, tana zuwa tayi sallama inna kota kallita ta aje kayan tallar tace inna ga kudin, humm munafika yau "ma har yayi maki juyen koh ? Aa inna yau an samu kasuwa ne , humm yarinya kenn ai nakusan kawo k'arsan wann wasan naku yarinya," bane kudina? Muhabbat ta bata kudin, ahankali tace Dan Allah inna intafe islamiyya? Inna ta yatsna fuska Wanda sai da ya baiyana mumunan fuskarnan tata, humm ai sai kitafe ai na San yau za suci ubanki munafika..

Tayi shrin islamiyya dama bata da uniform din islamiyya haka take tafiya tana zuwa ta zamu malam Umar a tsyi zata wuci ya kirata, yace muhabbat meya hanake zuwa islamiyya kwana biyu? Tayi shru yace ina tambayarki kinyi shru kawai ta fashe da kuka ahankali ya karaso kusa da ita yace muhabbat ya isa nasan matsalarki kawayenki sunyi man bayane komai wann alkawarin da na"daukarwa zuciya ta zan taimakeki kota halin Yaya insha Allah.....


Toh makaranta novel din MATAR MUTUM hameed yace zai taimaki muhabbat haka kuma malam Umar toh dukkansu ko wane taimako zasu bata.....


(08021084887)

Na MRS UMAR

MATAR MUTUM 41_45

[4/6,8:30.PM]BY FATIMA

MATAT MUTUM

. 41_45.

NA
MRS UMAR

ASALIN LABARINA SHINE

Malam Amadu shine Ai nahin sunan mahaifina ba wani mai kudi bane yana dai kasuwancinsa," yana da mata mai suna maryam wato inna mairo kenn mahaifina yana hakuri da inna mairo sosai, gashi suna da matsalar haihu kusan shakararsu 5 da aure amma Allah bai basu haihu bah, mahaifina yadamu kwarai da gaske haka mahaifiyar babana ta damu sosai wata rana har tazo tasamu inna amma inna tayi mata rishn kunya....

Mahaifina da yaji maganar baiji dadi bah amma yayi hakuri saboda yasan halin inna mairo kenn...
Wata rana mahaifina yaje kauyensu ranar tayi masa dadi saboda ranar ne yahadu, da "mahaifiyata mai suna fadima sunzo bikin wasu yan uwansu daga Cameron mahaifiyata ba yan Nigeria bace su fulanin Cameron ne ,anan ne mahaifina yaneme auren mahaifiyata..

Mahaifina yasha wahala kafin yasamu auren mahaifiyata sai da yabita har Cameron yan uwanta sukace bazasu ba kado auren yarsu bah, sai da suka ga ba sarki sai Allah sann suka basa aurenta ..

Inna tunda taji labarin baba zai kara aure hankalinta yatashi sosai ba inda inna bata shgaba, dan ganin an fasa auren amma abin yaci tura, haka mahaifiyata tazo gidan inna ta damita da wahala abin Allah bayan aurensu da wata uku Allah yabata ciki tunda inna taga cikin nan take safa da marwa wajan malamai da bokaye har sai da inna taga cikin nan yafita kafin hankalinta ya kwanta ba a jima bah tasake samun ciki sai dai wann salon ya chanza saboda ba yanda inna batayi bah Dan cikin yafita amma yak'i fita haka ta hakura har Allah ya sauki mamana lapia aka haifini...

Mahaifina tunda aka haifini yake nuna man so inna abin na bata haushi kamar zata mutu amma ba yanda zatayi, idan mahaifina yatafi kasuwa mamana takoma kamar baiwa wajan inna..

Inna duk wajan boka da taje Dan akashe mamana sai bokan yace bazai iya bah wata rana lami tazo tace mata tasamo mata wani sabon boka suka shrya sukaje wajan bokan tunda suka dawo gida mamana bata kara gane kan babana bah yazo ya tsnimu wata rana an waye gari ba mamana ba dalilinta hankalina yatashi sosai naje nasamu babana amma sai naga ko a jikinsa tunda ga ranar har yau bansa mamana a idoba kusan shakara 10 kenn saboda sann bani da da wayau sosai bayan tafiyar mamana kakata tazo daukata wato maman babana amma inna ta hana nayi kuka kamar ba gobe maganar da nake maka har yanxu yan uwan mamana basuzo sun tambaya ina take bah, babbar matsalata yanxu itace rashn ilimi toh kaji labarina.....

Hameed yayi ajiyar zuciya yace INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJU'UNNN dama har yanzu ana samun irin wa anan matan marasa imani a duniya ahankali ya kalleta dama tunda ta fara basa labari kanta a kasa tana kuka yace muhabbat please stop crying relex your mind I will help u muhabbat tace na am mekace.....


Toh ko wane taimako hameed zai bah muhabbat oho .......



(08021084887)

NA MMRS UMAR

MATAR MUTUM 36_40

[4/3,6:00PM]BY FATIMA

MATAR MUTUM

36_40

NA
MRS UMAR

Hameed yana cikin tunani sai ga minal ta shgo da sauri yadaga idonsa ya kalleta ta fada jikinsa kamar yanda tasaba koda yaushe, hameed yace please minal yau bana jin" dadi kibarni, yaya What is wrong with u? Humm I feel sick and tired please just go, ahankali ta kallesa tace yes yaya I will go, tafita tana fushi saboda minal tana son yayanta sosai.. Shi koma yace insha Allah sai na taimaki muhabbat Ku ta halin Yaya ...

Inna tana zaune ita da baba lami tana gaya mata abinda yafaru jiya da daddare, lami tace ai wann magana mairo ba ta bari bace ai wajan boka zamu kuma saboda idan har muka bari wann shgeyar yarinyar ta aure wann yaron shkenn kashinmu yabushe mairo,inna tace toh yanzu yaushe zamu koma wajansa?" ai ni ko yanzu in kin shrya mutafi kawai, aa mubari sai gobe da safe toh shkenn,, duk maganar nan muhabbat najinsu hankalinta ya tashi sosai tace na shiga uku kada su inna su kashe yaron mutane saboda basu da imani a ransu,,

Da sauri muhabbat ta karasu wajansu, tace inna nagama ina kayan tallar? Hummm munafika yau tun yanzu zaki dauki tallar toh Wallahi naganki ke da wannn yaron sai naci ubanki munafika, muhabbat tace toh inna....

Muhabbat ta dauki tallar Sauri take kamar zata tashi sama ba inda ta tsya sai inda su hameed ke zama tana zuwa tasamishi zaune da sauri ta k'arasa wajansa jikinta har rawa yake, tace Dan Allah malm mai taimako inaso nayi magana da kai, hameed yace lafiya dai koh? kawai sai muhabbat ta fashe" da kuka da sauri kamal ya taso yana shrin kamata, hameed ya sha gansa, yace what is this is it with u she said she want to talk? Kamal yace Yes what is your concern, hameed yayi tski yaja hannunta yasa a motarsa shima yashga itako kuka take kamar rainta zai fita..
KAMAL yaji haushi kamar ya mutu...

Ba inda hameed yatsya da muhabbat sai wani katan waje" inda mutane ke hutawa hameed yabude mata mota tafito sai yanzu muhabbat tabude idonta tunda tafara kuka bata bude idantabah sai yanzu, hameed yanuna mata inda zata zauna , " dukkansu suka zauna ahankali hameed ya kalleta yace please kanwata meke damunki? "Muhabbat takara fashwa da kuka mai cin rai ahankali hameed ya matso kusa da ita ya kama hannunta " yace please kidaina kuka ki gaya man me ke damunki? muhabbat ta kifa kanta a kafarsa tace nashi ga uku wallah akwai matsala hameed yace muhabbat matslar me yafaru ya dago kanta yana kallonta. tace naji inna tana fada ma baba lami wai zata kaika wajan boka kuma wallahi inna zanta iya yin komai Dan ta rabaka da duniya,, Dan Allah karka kara zuwa gidanmu, hameed yayi murmushi yace muhabbat kenn ai ba abinda inna ta isa tayi man bayan wanda Allah zai yi man dan haka ki kwantar da hankalinki inaso yau ki bani labarin rayuwarki.........da inna

(08021084887)

NA MMRS UMAR

MATAR MUTUM 31_35

[3/30,10:15.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM

31_35.

NA
MRS UMAR

Hameed yana mata wani irin kallo na tausayi cikin zuciyarsa yake cewa Ashe matar nan karya take fada man dama tana chutar yarinyar mutane gaskiya wasu mutane basa tsoron Allah, yana cikin wann tunani "yaji inna na magana tana cewa toh munafiki yau"ma ka biyo ta koh? toh wallahi baka isa'bah sai nashiga duk inda zan shga dan gane narabaku, hameed bai gane abinda take nufi'bah...

Ahankali ya kalleta yace mama I did not understand what u are saying, inna tace me kace munafiki turwa uwar turi"turi ta ture uwata sannu bature, hameed yace toh ni dai mama wallahi bansan menayi bah, inna tace munafiki kace baka saniba mana tunda kabiyota kusake shashancin ko, hameed ya zaro ido yace INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJU'UNNN.mama wallahi ni ba fasik'i bane, inna tayi murmushi takaici tace humm yaro yaro ne zata"jawo muhabbat hameed yasha gabanta cikin fushi yace wai ke wacce irin matace ana baki hakuri bazakiyi bah" eh bazanyi bah munafiki kawai toh wallahi ina gaya maka karabu da ita idan ba haka'bah duk abinda yabiyo baya kar"kai kuka da ni kayi kuka da kanka, hameed yayi murmushi yace mama kenn ai ni da Allah nadogara ba da mutum "bah inna tace aikin banza kawai tashge gida ai yarinya zakizo ki sameni..

Hameed ya juyo muhabbat ahankali a bansa yadago kanta yafara Shari mata hawayen idonta yace is alright stop crying kiyi hakuri duk mai hakuri yana tare da Allah so ni bansan abinda" ke faruwa dake kenn' bah dama nazo in gaya maki duk ranar da kamal yace ku had'u a wani waje please kar kije kinji koh? ahankali muhabbat ta dga masa kai tace toh, yace yauwa kanwata kiyi hakuri insha Allah zan dinga zuwa ina dubaki kinji koh? eh, hameed ya zaro kudi masu yauwa yabata yace ga wann ki shga gida muhabbat tace aa wallahi nagode,, yace haba ai ni nabaki Dan haka ki amsa, tace toh shkenn na gode, toh" but idan kinshga duk abinda za ayi maki kiyi hakuri please ,"cikin muryar kuka tace toh nagode...

Hameed ya nufi motarsa yashga ita kuma gida tashga, Ashe inna tana labe zaure duk tana jinsu muhabbat nashga inna tace munafika bani kudin da yabaki, da sauri ta bata inna tadaka mata tswa tace daga yau kada na sake gann wann munafikin a gidan nan kinaji koh? eh inna tace shgeya munafikar banza , sai kije ki zauna ahankali muhabbat tashga ta zauna....

Hameed har ya isa gida yana tunanin halin da yabar muhabbat dakinsa ya nufa dama lokacin sallah yayi sai yanufi, toilet dan yin alwala bayan yagama yin alwala yazo yayi sallah sann yayi adduar da yasaba kullum ...

Kan kujera yakuma ya kwanta yana tunani a cikin zuciyarsa yake magana a gaskiya ina mai tausayin wann yariyar abinda yabani tsoro game da ita ga Dr yace man tana da hauwan jini toh wane taimako yadace nabata, gashi kuma yariyar bata cikin jerin matar da nake so na aura.....

Saturday, 7 May 2016

MATAR MUTUM 26_30

[3/29,10:45.AM]BY FATIMA

MATAR MUTUM
.
. 26_30.

NA
MRS UMAR

WAYE HAMEED DA KAMAL

Alhaji abubakar mai changi shine ai nahin mahaifin hameed Babba mai kudi ne a cikin garin Katsina Wanda yaro da Babba yasansa alh abubakar matarsa daya wato mahaifiyar hameed mai suna saratu alh abubakar iyayensa sun rasu tun yana yaro sakamakon hatsrin mota haka alh abubakar ya taso komai nasa shi daya har Allah yasa yagama karatunsa a A.B.U ZARIA yafara changin dollars har Allah ya hadasa da Hajiya saratu alh abubakar yasha wahala kafin samu auren saratu saboda mahaifansa basa duniyar haka har Allah yasa aka daura masu aure inda ya gina gidansa a G R A bayan sunyi aure da wata uku Allah ya albarkacisu da juna biyu haka saratu tasha wahala kafin Allah ya sauketa tafiya inda ta haifi kyakkyawan saurayinta, ranar suna yaro yaci sunan ABDUL HAMEED bayan shakara biyar hameed yayi wayau aka sashi primary achan ne suka had'u da KAMAL suka shaku sosai yanda har takai iyayensu sunsan abotakansu bayan shakara sheda suka gama primary dukkansu sukace sai dai a hadasu makaranta daya haka aka sasu a secondary bayan shakara 10 saratu tasake haihuwa yarinya mai suna minal,haka su hameed suka gama secondary inda mahaifin kamal da hameed suka zauna sukayi magana inda zasu kaisu makaranta ta gaba da secondary wato Nigeria Defence Academic wato (N D A) Kaduna sai da sukayi shakara biyar sannn suka gama suka fito cikakken Nigeria army inda suka fito a matsyin second leftanant haka akayi posting dinsu Barrack daya a garin port Harcourt wato bori camp barracks sai dai halin kamal da hameed ya bambanta saboda shi kamal ma abaucin son mata ne shikuma hameed baruwansa da kowacce mace aikinsa kawai yake yanzu an basu hutu sunzo AREWA .........

Hameed gida yanufa yana zuwa yasamu su dady da mom zaune a falo suna fira ya gaishesu ya wuce dakinsa bedroom ya wuce ya fada kan gado yana tunani wata zuciyar tace tunda yasan gidansu yarinyar yaje kawai haka yafito ya hau motarsa sai gidansu muhabbat.....

Muhabbat yau tadawo inna sai masifa take wai yau bata sayar da tallarbah tace wlh inna yau garin ba kasuwa, ba kasuwar ubanki munafika inna tabiyo muhabbat da gudu Ashe hameed na tsyi a soro yana jinsu muhabbat da gudu tayi tutube zata fadi sai ta fada jikin hameed kawai sai jinta tayi cikin k'irjin hameed Ahankali hameed ya dago kanta yana mata wani irin kallo.....

Toh jama a wani kallo hameed ke ma muhabbat kallo so ne ko na me?

Bari muga wazai bamu amsa....

(08021084887)

NA MRS UMAR

MATAR MUTUM 21_25

[3/26,12:30.PM]BY FATIMA

MATAR MUTUM

21_25.

NA

Wednesday, 4 May 2016

MATAR MUTUM 16_20

[3/24,7:30.PM]by Fatima

MATAR MUTUM

16_20.

NA
MRS UMAR

Hameed ya rukota ta fada jikinsa cewa yake SUBHAAN ALLAHI pls mike damunki ina ai muhabbat har ta sama,, da gudu yasata a mota sai asibiti kai tsyi ALLAH BAMU LAFIYA yawuce da ita direct" yana zuwa yayi sa a akwai Dr akayi Sauri aka shga da ita hameed ya dade tsyi sannn sai ga Dr ya fito da sauri hameed ya isa wajansa yace pls Dr Mike damunta? Dr yayi ajiyar zuciya..

Gaskiya nayi mamakin ace yarinya kamar wannn jininta yahau har kusan 150 what hauwan jini kuma? Eh wallahi abinda report ya bada kenn, toh Dan Allah Dr you should try Best so that she will get well , " yes i will try my best ..
Yauwa Dr nagode yanzu zan iya zuwa ganinta? eh muji kaganta suna zuwa suka samu muhabbat na kokarin tashi da Sauri hameed ya rikita, ahankali ta kallishi tace malm kai waye? hummm I am a human being yanzu dai Mike damunki? Bakumi, ke kanwata Allah bakumi,,

Dr yanxu zamu iya tafiya gida koh eh zaku iya tafi amma don Allah a dinga bata magani kuda wane lokaci insha Allah Dr,, za'a bata amma Dr yanxu ba abinda ke" damuta koh? Eh gaskiya babu sai dai kawai ciwon mara amma wannn ba problem bane kawai dai dukka wata dole tayisa,, toh Dr thank u so much...

Hameed ya ruko hannunta ya isata mota tunda suke tafiya ba wanda yace" ma wane kalla sai yanzu hameed ya juyo ya kallita yace ina ne gidanko? ai ni ba gida zanjibah toh ina zakije talla what talla da wannn jikin nake? eh OK naji toh yanzu wacce unguwa kike ina kofar kaura, yanxu har kofar kaura kike zuwa talla har nan eh,,

Tunda hameed ya tambayita unguwarsu bai sake mata magana"bah muhabbat taga yajuya kan motarsa ya nufa titin kofar kaura tace nashi ga uku ina zaka kaini ban sayar da tallar bah yaju ya kallita fuska a daure yace gidanko don Allah karufaman asiri in tafi tallana hameed ko kallanta bayi bah kayi muhabbat ta fashi da kuka Ko kalla hameed baice matabah sai da suka isa kofar kaura sannn yace...

Pls malama idan kin gama kukan Ina"ne gidan? ni nace maka ba gida zanjibah OK naji dukka kayan tallar na nawa ne na 400 OK toh zan biyaki...
Yanzu ina ne gidan gashi chn OK hameed yana parking motarsa muhabbat ta fito da sauri, toh mu shga koh aa nidai ban yarda"bah zanshga ni daya aa inaso muyi magana da babanki ai babana baya nan yaji kasuwa,, OK toh kiyi man magana da mamanki; muhabbat zata bude bak'i tayi magana kenn taji inna na cewa wai suwaye anan hameed yace mune kusuwa? Baku'ne toh shgo hameed yayi sallama inna ta amsa masa sannu da zuwa Baku mukayi gidanamu?,eh wlh toh ga kujera hameed ya zauna sai da suka gaisa sannn, " hameed yace dama ina cikin tafiya ne da mota na had da wannn yarinyar ba lafiya toh nan dai ta fade na daukita na kaita asibitin daga karshe dai Dr yace wai tana dauke da hauwan jini, hauwan jini na shga uku dama " ebba bakida lafiya baki gaya man bah " Dan muta ne su zage ni"wlh Ebba wlh kisake hali Allah nagani ina zaune dake tskani da Allah kawai inna sai aka fashi da kuka,, hameed yace toh yanxu dai ga maganin da suka ba ni nan a dinga bata don Allah mama a din ga bata su kan lokaci " haba ai bakumi za a bata.toh shkenn ni" zan kuma duk sanda nasamu lokaci zan dinga zuwa aa wlh bama sai kazo bah" haka" ma mungode toh shkenn ga wannn asai guro aa wann kudi haka...
Mama kenn ai ba yauwa, toh nagode yaro Allah yayi albarka ameen toh sai anjima toh ka gaida gidan yauwa albarka ki rakasa mana toh inna muhabbat tayi mamaki yanda inna ta sauya halinta sa"i daya har jikin motarsa ta rakasa ahankali muhabbat ta kallisa tace nagode hameed yace bakumi but ya kata idan baki da lapia ki gayawa mamanki kinji koh eh naji yauwa ga kudin tallar ki aa ai naga kaba inna aa wannn kyuta nabata toh nagode,,

but ya sunanki sanna MUHABBAT amma inna na kirana da Ebba OK yayi kyau,, toh kai ya sunanka hummm ni sunana mai TAI MAKU DAN ALLAH......


(08021084887)

MRS UMAR

MATAR MUTUM 11_15

[3/20,12:00.AM] by Fatima

MATAR MUTUM
.
11_15.

NA
MRS UMAR

Dukkansu sun fito amma banda"hameed dady yadube, mom yace Hjy yau ina hameed yake "ne bai fitoba? Wlh alh nima bansaniba dady dube minal yace minal go and call me hameed , OK dady.

Assalamu alaikum yaya oh my God wai minene minal dama Yaya dady ne ke kiranka; OK kice mai ina zuwa"toh Yaya what are u doing,? Kabude man kofa mana, ohhhh Milan I am doing something,,because inaso naji wani waje.. Pls yaya whare are u going? Wai ke wacce irin yarinyaci mai tambayar tsya" nace maki ina zuwa aa,, toh Yaya am sorry, toh naji jeki zanzo yanzu.. Yaya zanci zakaji ne ? bansani'bah minal karfa kibari nafito wajan nan hameed na kukarin bude kofar daki minal ta ruga ...

Sae da hameed yagama shrensa sannn yafito, yasamu su dady da mom zaune suna breakfast shima ya zauna kan kujera da yasaba zama kuda yaushe, dady good morning" Morning my son how are u? Fine dady,, sannn ya'juya ya kalli mom yace mom ina kwana"lapia qlau ohh nida hausa za'a gaishni kenn? Dady yayi dariya yace in banda abinki ai ke bahausaci,, hhhhh kukuma gaku turawa koh aa mom ba haka yake nufi"bah, toh miyake nufi. yana nufin muyanzu munsaba zaman cikin turawa, koh eh mom toh . shkenn mubar maganar....

Suna cikin cin abinci dady ya dube hameed yace wai hutun kwana nawa aka baka ne? wlh dady two week ne kawa, ai sunyi kukari ma but before you go you need to marry bana son kana zama ba mata kusa da kai, dady am sorry you need to give me time because har yanzu ban samu Matar aure bah OK" zan baka amma gaskiya nake gaya maka;, nasani dady insha Allah zan samu toh Allah yayarda dukkansu sukace ameen hameed ya tashi ya shga dakinsa minal tabisa tana mai dariya yaya an kusan zama ango da gudu ya biyo ta......

YAU TAKAMA RANAR ASABAR
Muhabbat tatashi da matsnanci ciwon ciki inna tana fitowa tace wannn kayan tallar ubanwa kika banma su,? wlh inna yau bani da lapia,, me, baki da lapia? Toh Allah yasa mutuwa kike wallahi sai kinji tallar nan yar bakinciki ohh so kike kibarman tallar nan toh wallahi sai kinjita munafikar banza mai mugun hali...

Muhabbat tatashi a haka ta dauk'i tallar nan haka tafita gida ga ciwon cikin da takeji kamar zata mutu ga jeri ga amai,,, tana cikin tafiya ahankali tana tunanin halin da take cikin (horn) din da taji a nayi ne yasata , dawowa daga tunanin da take" Wanda ke cikin motar ya fito cikin fushi yace ke wacce irin yarinyaci ana maki horn bakiji,, yana cikin magana muhabbat kawai ta wane lummmm zata fadi yayi Sauri ya rukuta.......


(08021084887)


MRS UMAR

MATAR MUTUM 6_10

[3/15,6:30.AM] by Fatima

MATAR MUTUM
.
6_10.

NA
MRS UMAR

Toh inna amma lokacin islamiyya yayi kuma malm Umar yace idan banje bah fa yau sae ya dakeni, rufe man baki munafikar banza ai keda samun karatu har abada sai dai kiga wasu nayi amma badai kebah,..

Suna cikin wannn maganar sai ga baba lami ta shigo wato kanwar inna itama tana shgowa ko tayi sallama kawai sai cewa tayi kinanan kina fama da wannn shgeyar koh? Humm "ke dai bari Yar uwa ai wannn muguwar yarinyar bazata bar munafinci bah irin na uwarta shgeya"tashi kibane waje kina kallona da manyan idanuwa kamar mujiya,, lami ta kwashe da dariyar mugunta..

Ahankali muhabbat tanufi toilet don in alwala dama batayi sallah la'asar bah bayan ta fito tana cikin alwala inna tazo da sauri ta kwasheta da mari tace don ubanki talla kenn? Cikin kuka muhabbat tace aa dama inna inaso nayi sallah ne sai in tafi, sallahr ubanki munafika, haka muhabbat ta dauki tallar nan tafita...

Kai Yar uwa kuto.kuto mugun ice yaro bai baneba balli ya raba wane mutum yaja dake ya kwana kiyama ai ko aljani sai yashirya make ke'ke sawa ayi don uban mutum kubayaso sama_sama dai Yar uwa,, kai lami kidaina zugani da yauwa ai kinsan wallahi yanda na raba uwarta da garin nan toh itama haka zan rabata dashi har abada amma kafin nan sai ta gama nemaman duniya ai shyasa idan zata talla bana barin ta fita da dati jikinta sai tayi wanka saboda tayi kasuwa da Sauri...

Lami ta kwashe da dariya tace ai na sanke ba wasa, yaushe zamu kuma wajan boka tsega don kinsan aikinsa naja? Hummm ai nizan gaya make aikin boka tsega naja saboda yanzu dukkan abinda nace wa malm a gidan nan toh ya zauna hhhhhhhhhh kai amma wallahi kinyi sa a shyasa nake sonki Yar uwa....

Humm kedai bari kawai ai ni wallahi dukkan Wanda yace zaija dani toh wlh zai kwana k'iyama bah shri ,, toh yanzu dai ranar asabar zamuji wajen bokan koh? Toh Allah yakaimu ameen, bari nayi neyar gida dare nayi nabar yara a gida toh shkenn sai ranar asabar din kenn eh toh kigaida gida toh gida zaiji....

Zaune suke saman (Dinning table) cin abinci wanda su hudu kawai ke zama kansa mahaifinsu sai mahaifiyarsu sai hameed da kuma kanwarsa minal....

(08021084887)

MRS UMAR

MATAR MUTUM 1_5

.[3/13,7:50.PM] by fatima

MATAR MUTUM

1_5.

NA
MRS UMAR

Ahankali take tafiya dauke da tirin talla a kanta cikin sanyin jiki da alama tunani take yanayenta zai sa kagani nutsatseyar yarinya ci bakin titi take tafiya wasu samari na zaune a bakin wani shagon kaya daya daga cikinsu yace kai jama a kudube wata yarinya a "can yarinyar her is beautiful dukkansu suka dubeta but banda mutum daya..

wanda yayi maganar, shiyasake magana yace kai kunsan matsalar yarinyar nan kuwa ?dukkansu sukace aa ..but banda dai dayan saurayin nan, yace matsalarta daya ce because ita sojan tirici dukkansu sukasa dariya ahankali naga ya dube saurayin nan da baya magana yace look my friend kuwa na magana kayi shiru sai yanzu yadaugo kanshi ...

ya salam wane kyakkyawan saurayi nagani wanda bazai wuci shakara 28 bah, cikin isa ya fara magana yace so what ina ruwana da"ita mai surutun nan yace haba HAMEED listen to me yarinya nan nada kyau fa sosae,hameed cikin fushi yace kamal pls just keep quite u will never understand me nagaya maka banason magana wata mace anan, hameed ya tashi yashiga motarsa kuya kalli idan yarinyar nan take yaja motarsa yayi gaya..

kamal yace yan mata zumana tace toh ahankali ta karasu wajansu ta ajiyi masu tirin tallai kamal yace nawa nawa tace goma goma yace toh kafin aci miyi sunanke? tace ne malam bani da suna, yace da gaski ta murguda mai baki tace eh.yace kai amma kinyi kyau fa tayi shru abinta yace pls yan mata Tell me u name" tace na'am mikace yace oh bakiji abinda nafada bani? Tace eh..

Kamal yace oh am sorry I am familiar with English tace an daba kuma, yace koh tace eh yace toh mubar maganar don Allah yaya sunanki? badan niba don Allah, tayi shru yace kubaki kaunar Allah ni tace aa ina kaunarsa mana yace toh gaya man tace sunana.....

Sunana MUHABBAT... tana ambatar sunanta sai da kirjin hameed ya buga yana cikin driven motarsa da Sauri ya'am baci sunnan Allah ..

Kamal yace wow suna mai dadi tayi murmushi wanda yabaiyana kyaunta muhabbat kyakkyawaci son kuwa kin Wanda bai samuba yarinya da atattarta bazata wuci shakara 15 bah macece har mace ga idanuwa ga hanci ga dukiyar Fulani wlh kuke mace in kika ganta sai kin sota don kyanta she is beautiful..

Kamal yace toh inaso nazo gidanku nakawu maki ziyara yaya za'ayi yanzu hummmmm ai ne gidanmu ba abarina fira da kuwa toh miyasa wlh bansaniba toh ko an maki mijini? aa wlh kai malm wlh kacika tambaya kamar dn jarida, au bakisaniba ai dn jarida kike tari dashi toh naji ni zan tafi talla yamma nayi, kar ki damu zan saye dukka ayar da gyadar yanzu duk tiri dn nawa muhabbat tace dukka ta dari 300 ci OK kamal yazaro five hundred yabata tace ai banida chnji badamuwa nabarmaki toh nagode yawwa ina zan zuba maka aa kiji dashi kiba yara sadaka aa dama badashi zakaba? eh, toh nagode kamal yace toh yanxu sai yaushe kenn? sai gobe insha Allah, OK Allah yakaimu toh ameen ki gaida gida toh amma kai ya sunanka aa sai kinzo gobe zan gaya maki toh Allah yakaimu ameen...

Ahankali muhabbat ke tafiya a nutse har takai wata kwana ta karya wani gida tashga tana zuwa ko sallama batayiba, naji wata masifafiyar mata ta tashi tsyi da balai toh shigeya har kin dawo daga talla baki sarba koh? ahankali muhabbat ta karasa wajanta tace aa babba dama wani mutum yasaye dukka yace naba yara sadaka hummm munafikar banza in'ma yawn gantalinki kikaji ina ruwana nidai bani kudin nan kuma in anjima ki daukita sai kin sai dota shgeya mai manyan idanuwa kamar na uwarta....


(08021084887)

MRS UMAR

About Fatima Umar

Placeholder for About Me page of Fatima Umar

Hello World!

Welcome to MyWapBlog.com. This is your first post. Edit or delete it, then start blogging!