Wednesday, 11 May 2016

MATAR MUTUM 36_40

[4/3,6:00PM]BY FATIMA

MATAR MUTUM

36_40

NA
MRS UMAR

Hameed yana cikin tunani sai ga minal ta shgo da sauri yadaga idonsa ya kalleta ta fada jikinsa kamar yanda tasaba koda yaushe, hameed yace please minal yau bana jin" dadi kibarni, yaya What is wrong with u? Humm I feel sick and tired please just go, ahankali ta kallesa tace yes yaya I will go, tafita tana fushi saboda minal tana son yayanta sosai.. Shi koma yace insha Allah sai na taimaki muhabbat Ku ta halin Yaya ...

Inna tana zaune ita da baba lami tana gaya mata abinda yafaru jiya da daddare, lami tace ai wann magana mairo ba ta bari bace ai wajan boka zamu kuma saboda idan har muka bari wann shgeyar yarinyar ta aure wann yaron shkenn kashinmu yabushe mairo,inna tace toh yanzu yaushe zamu koma wajansa?" ai ni ko yanzu in kin shrya mutafi kawai, aa mubari sai gobe da safe toh shkenn,, duk maganar nan muhabbat najinsu hankalinta ya tashi sosai tace na shiga uku kada su inna su kashe yaron mutane saboda basu da imani a ransu,,

Da sauri muhabbat ta karasu wajansu, tace inna nagama ina kayan tallar? Hummm munafika yau tun yanzu zaki dauki tallar toh Wallahi naganki ke da wannn yaron sai naci ubanki munafika, muhabbat tace toh inna....

Muhabbat ta dauki tallar Sauri take kamar zata tashi sama ba inda ta tsya sai inda su hameed ke zama tana zuwa tasamishi zaune da sauri ta k'arasa wajansa jikinta har rawa yake, tace Dan Allah malm mai taimako inaso nayi magana da kai, hameed yace lafiya dai koh? kawai sai muhabbat ta fashe" da kuka da sauri kamal ya taso yana shrin kamata, hameed ya sha gansa, yace what is this is it with u she said she want to talk? Kamal yace Yes what is your concern, hameed yayi tski yaja hannunta yasa a motarsa shima yashga itako kuka take kamar rainta zai fita..
KAMAL yaji haushi kamar ya mutu...

Ba inda hameed yatsya da muhabbat sai wani katan waje" inda mutane ke hutawa hameed yabude mata mota tafito sai yanzu muhabbat tabude idonta tunda tafara kuka bata bude idantabah sai yanzu, hameed yanuna mata inda zata zauna , " dukkansu suka zauna ahankali hameed ya kalleta yace please kanwata meke damunki? "Muhabbat takara fashwa da kuka mai cin rai ahankali hameed ya matso kusa da ita ya kama hannunta " yace please kidaina kuka ki gaya man me ke damunki? muhabbat ta kifa kanta a kafarsa tace nashi ga uku wallah akwai matsala hameed yace muhabbat matslar me yafaru ya dago kanta yana kallonta. tace naji inna tana fada ma baba lami wai zata kaika wajan boka kuma wallahi inna zanta iya yin komai Dan ta rabaka da duniya,, Dan Allah karka kara zuwa gidanmu, hameed yayi murmushi yace muhabbat kenn ai ba abinda inna ta isa tayi man bayan wanda Allah zai yi man dan haka ki kwantar da hankalinki inaso yau ki bani labarin rayuwarki.........da inna

(08021084887)

NA MMRS UMAR

No comments:

Post a Comment