Wednesday, 4 May 2016

MATAR MUTUM 6_10

[3/15,6:30.AM] by Fatima

MATAR MUTUM
.
6_10.

NA
MRS UMAR

Toh inna amma lokacin islamiyya yayi kuma malm Umar yace idan banje bah fa yau sae ya dakeni, rufe man baki munafikar banza ai keda samun karatu har abada sai dai kiga wasu nayi amma badai kebah,..

Suna cikin wannn maganar sai ga baba lami ta shigo wato kanwar inna itama tana shgowa ko tayi sallama kawai sai cewa tayi kinanan kina fama da wannn shgeyar koh? Humm "ke dai bari Yar uwa ai wannn muguwar yarinyar bazata bar munafinci bah irin na uwarta shgeya"tashi kibane waje kina kallona da manyan idanuwa kamar mujiya,, lami ta kwashe da dariyar mugunta..

Ahankali muhabbat tanufi toilet don in alwala dama batayi sallah la'asar bah bayan ta fito tana cikin alwala inna tazo da sauri ta kwasheta da mari tace don ubanki talla kenn? Cikin kuka muhabbat tace aa dama inna inaso nayi sallah ne sai in tafi, sallahr ubanki munafika, haka muhabbat ta dauki tallar nan tafita...

Kai Yar uwa kuto.kuto mugun ice yaro bai baneba balli ya raba wane mutum yaja dake ya kwana kiyama ai ko aljani sai yashirya make ke'ke sawa ayi don uban mutum kubayaso sama_sama dai Yar uwa,, kai lami kidaina zugani da yauwa ai kinsan wallahi yanda na raba uwarta da garin nan toh itama haka zan rabata dashi har abada amma kafin nan sai ta gama nemaman duniya ai shyasa idan zata talla bana barin ta fita da dati jikinta sai tayi wanka saboda tayi kasuwa da Sauri...

Lami ta kwashe da dariya tace ai na sanke ba wasa, yaushe zamu kuma wajan boka tsega don kinsan aikinsa naja? Hummm ai nizan gaya make aikin boka tsega naja saboda yanzu dukkan abinda nace wa malm a gidan nan toh ya zauna hhhhhhhhhh kai amma wallahi kinyi sa a shyasa nake sonki Yar uwa....

Humm kedai bari kawai ai ni wallahi dukkan Wanda yace zaija dani toh wlh zai kwana k'iyama bah shri ,, toh yanzu dai ranar asabar zamuji wajen bokan koh? Toh Allah yakaimu ameen, bari nayi neyar gida dare nayi nabar yara a gida toh shkenn sai ranar asabar din kenn eh toh kigaida gida toh gida zaiji....

Zaune suke saman (Dinning table) cin abinci wanda su hudu kawai ke zama kansa mahaifinsu sai mahaifiyarsu sai hameed da kuma kanwarsa minal....

(08021084887)

MRS UMAR

No comments:

Post a Comment