Tuesday, 12 July 2016

MATAR MUTUM 111_115

[5/9,4:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM

.
111_115

NA
MRS UMAR


Mom wayarta ta dauka ta d'ana number Hameed cikin sa'a kira d'aya ya daga wayarshi cikin girmamawa yayi sallama. "Ina kwana mom? Lafiya Qlau Hameed ka tashi lafiya. " lafiya Qlau mom. "Toh dama abinda yasa na kiraka wai yanzu Kamal ke gaya man zai koma wajen aikin shine na tambayishi nace toh ina kake da zai tafi shi d'aya don Allah ka gaya man ko k'arya yake. " Hameed yayi shru ya tunani wace amsa zai ba mom sai can d'ubara tazo masa yace. "Eh Mom nasani zai tafi ni abinda yasa banbisa bah, saboda maganar auren nan but ba wata matsala mom. " toh shkenn Hameed Allah yayi maka albarka. "Amin mom toh sai anjima.

"Ai kam dama k'irjin kamal sai dakan uku_uku yake yana tunani ko Hameed zai gaya ma mom abinda ya faru, sai gashi bai gaya mata bah, haka ya gama had'a kayanshi sannan ya kama hanyar garin Port....

************
Hameed ne zaune shida Muhabbat suna fira d'in zaman da sukai da junansu ya k'ara sa masu soyayyar juna,Hameed ya kalli Muhabbat yace " so ya kamata Dr ya sallameki saboda maybe yau su dady zasuje gidanku so yanzu bari nayi ma Dr magana, koh ya? Amaryarta. "Muhabbat tayi murmushi ta rufe fuskarta da hannuwanta, shima haka yayi murmushi ya fita wajen Dr,,
Bai jumabah sai gashi ya dawo,yana zuwa yace" ta taso su wuce gidan,haka suka nufi gidan suna zuwa suka hadu da Abba dai_dai lokacin da zai d'auki kekenshi ya fita cikin sauri Hameed yayi parking tare suka fito shida Muhabbat,cikin girmamawa ya gaida Abba sai da suka gama gaisawa kafin Hameed ya fara yimasa maganar abinda ya kawoshi yace, "dama Abba Dr ya sallamemu kuma dama mahaifina yace nagaya maka yau insha Allahu za'a kawu kud'in neman auren Muhabbat. " Abba yayi shru na wani lokaci sannan ya dube Hameed yace, "toh yaron bazancemaka eh ba kuma bazance a'a bah dan haka sai na shiga nayi ma mahaifiyarta magana idan ta aminci toh shkenn idan bata aminci bah, toh sai dai kayi hakuri.
"Hameed yayi shru yana tunani maganar Abba, anya kuwa Abba Inna zata barshi ya aminci da maganar auren nan, toh Allah gamu garika duk cikin zuciyarsa yake wannan maganar,cikin murya kasa kasa yace," toh Abba kashga ka gaya mata ina nan ina jiranka kafito. "Abba bayi magana bah yajuya yashga cikin gida,yana zuwa ya samu Inna zaune a tsakar gida Muhabbat na gefinta zaune,Abba ya tsguna gaban Inna kamar mai neman ga fara yace " mairo dama yaron nane yazo man da wata magana wai yanaso ya aure Muhabbat shine nace mashi toh bari nazo na gaya maki idan kin aminci shkenn. "Inna tayi shru sai can ta tuna wani abu sai tayi murmushi tace, " Kai madalla abu yayi kyau toh yaushe zasuzo? "Yace man kamar yau zasuzo. " toh ai tafiya kasuwa ya faso, sai ka bari suzo.
"Abba yace toh shkenn bari na gaya mashi suzo, inda yabar Hameed zaune nan ya sameshi nan yace mashi bah matsala suzo, Hameed yayi murna sosai, sannan yashga motarshi ya tafi tun yana mota yakira dady ya gaya mashi.....

Haka su dady sukaje gidansu Muhabbat gaskiya bah laifi Abba yayi masu tarba mai kyau nan suka yanke shawarar bikin nan da wata biyu masu zuwa insha Allah!!!!


®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment