[5/15,7:50.PM]BY FATIMA
MATAR MUTUM
.
131_135
NA
MRS UMAR
Suna cikin mota Hameed ya
d'auki wayarshi ya kira dady ya gaya mashi koda dady yaji haka, hankalinshi yatashi sosai amma Hameed sai yanuna mai ba wata matsala sudai tayashi da addu'a kawai, dady yaba mom haka itama tayi mashi addu'a sosai, sannan ya kira Minal yace maza ta kaima Muhabbat zayi magana da ita, Minal bata bata lokaci bah ta isa gidansu Muhabbat tayi sa'a bata fita talla bah, Minal tayi sallama Muhabbat ta amsa, tayi mamakin ganinta, sai da suka gaisa kafin ta danna wayarta ta kira hameed, ringin d'aya ya d'aga Minal tayi sauri tabah Muhabbat haka ta amshi wayar yau ce rana ta farko da Muhabbat ta fara riki waya.....
"Hello Muhabbat kina jina yakk? "Eh Yaya ina jinka lafiya Qlau ya aiki? " lafiya Qlau matata da fatan baki tare da wani problem, so idanma kina da Matsala kiyi ma Minal magana zata gaya man, sannan magana ta biyu yau zamu wuce Maiduguri, inaso ki tayani da addu'a Allah yamaidumu lafiya kinji my wife....
"Inda Muhabbat ke tsye nan tayi mutuwar tsye sai hawaye kawai ke fita d'aga idonta Hameed shrun yaji tayi yauwa ahankali ya rage murya yace "Muhabbat kuka kike kinaso natafi cikin bacin rai, bakya so na tafi ina tunanin kyakkyawar fuskarki, haba Fulani matata kuma uwar yayana insha Allah sai kunga yayanmu nidaki, don Allah kiyi man magana ko zuciyata zatayi sanyi. "Wata irin ajiyar zuciya tayi saboda yanda tayi ajiyar zuciyar sai da tsigar jikin Hameed tatashi saboda har cikin kanshi tashiga saboda da a gabanshi tayita toh gaskiya da anyi abu.......
" toh Yaya Allah yatsre hanya yabada sa'a amma Yaya inajin wani Abu a jikina Yaya kamar in katafi bazaka dawo bah. "Haba Muhabbat ya kike irin wannan magana, addu'a kawai nake buk'ata kinji koh? "Toh Yaya Dan Allah idan kaji ka dunga tunawa dani. " oh my wife abinda yazama dole, insha Allahu bikinmu saura sati biyu zandawo naga matata daga nan in anyi bikin zan maidake makaranta. "Da Gaske yaya? "Allah, so yanzu zan barki mutane najirana sai munyi waya zan kira Minal sai ta kawu maki. " toh Yaya nagode. "Haka Hameed ya kashe wayarshi yana mai tunani Muhabbat dinshi, mutane duk sun taro, kusan sojjoji guda 100 aka kwasa zuwa Maiduguri kuma duk Hameed ni ogansu shi zai kulla dasu, ahankali kamal bai tafiba saida yaga su Hameed suntashi, yayi kuka kamar ba gobe, saboda yaso ace shi akasa bah Hameed bah....
Muhabbat sundanyi fira da Minal kafin ta rakata har bakin titi bayan fitarsu Inna tayi dariya sosai tace " ai yanda ka tafi Maiduguri toh, insha Allahu sai dai a kawu gawarka, garin nan....
GARIN MAIDUGURI
su Hameed sun sauka garin Maiduguri lafiya inda aka d'aukesu aka kaisu wani kauye a DAMBUWA kauyan na kusa da bodar Cameron, nan fa suka yada zango..
Washe gari
Inna sai gidan Lami dan ta bata ruhuto, Inna tace lalle lalle yau sai sun kuma wajen boka dan kar Hameed yakai labari, haka sukaje wajen boka, yayi masu albishir da shiyasa aka kai Hameed Maiduguri, kuma Hameed ya gama rayuwa a duniya....
"Hummm boka kenn ai ka manta bakai bane Allah kuma MATAR MUTUM kabarinshi idan Allah yace Muhabbat matar Hameed ce ba Wanda ya isa yahana,
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment