[5/14,7:00AM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
.
126_130
NA
MRS UMAR
Bayan dawowar Hameed falo kenan sai ga kiran dady ya shgo, a wayarshi da sauri ya d'aga cikin girmamawa. "Hello dady ina wuni? Lafiya Qlau my son, ya kun isa lafiya? " lafiya Qlau dady ya mom? "Gata a kusa dani. " sai da dady yaba mom suka gaisa kafin ya kashe wayarshi,Hameed yayi addu'a ya kwanta bacci...
Washe gari
Bayan yadawowarshi daga mallaci sallahn asuba, bai koma ya kwanta bah kitchen ya nufa direct yasa ruwan zafi, sannan ya shga bedroom, dan ya dn watsa ruwa saboda yau zai koma aiki, yana shga ya samu kamal ko juya kafad'a bayi bah, Hameed ya girgiza kai yace"Allah yashiryika, asuba tayi but mutum bazai iya tashi yayi sallah bah. "Hameed Kawai ya shiga toilet abinshi, sai da har Hameed ya kusan gama shirinshi kafin kamal ya tashi daga bacci,
Hameed ruwan tea kawai yasha ya d'auki key din motashi ya fita, kamal cewa yake, " a'a katsaya mana nima nagama mufita tare "Ai Hameed baima san yana yiba, yashga mota yayi tafiyarshi office,
Yana zuwa office yasamu har ancika saboda yau antashi garin MAIDUGURI ba lafiya , yanzu yanzu za'a kwashi sojjoji zuwa maiduguri, yana zuwa commanda, yace, "yauwa major Hameed kai zaka wuce dasu zuwa maiduguri because no one can do this work like u, aikin nan dole sai kai Hameed, but yau d'in nan zaku wuce.
"Allah sarki Hameed yana yinshi har ya sauya yace "am sorry sir duk ga manya nan sir ai ya kama asa wani wanda zai kulla dasu. " Hameed are u mad? ina magana kanace min, a'a so ba wanda zansa , sai kai because riqo da addininka yasa har na tabbata zaka kula dasu kuma yanzu maza ka koma gida ka had'a kayanka kuwuce yau d'in nan!. "Ogansu yana gama magana yajuya yafita, sojjojin da aka zab'a zuwa maiduguri sukasa ihu sukace. "Yauwa munji dad'i da aka had'amu da major Hameed because zai bamu goyan baya d'ari bisa d'ari. " Hameed kasa magana yayi saboda haushe, gashi d'aga dawowarshi, jiya, jiyan, nan, gashi yanzu har ansa sunanshi zuwa Maiduguri, ga maganar aurenshi da Muhabbat, hawaye da zasu zobomashi yayi sauri ya sharesu, wata Zuciyar tace. "Haba mazan fama kada kaba maza kunya mana kaifa jarimine. "Fitowa yayi ya d'auki motarshi ya koma gida, har yanzu kamal bai gama abinda yake bah, yana zuwa yasamu kamal kan kujera yana sa bot dinshi, Hameed naso ya gaya mashi amma ya kasa, bedroom ya nufa ya d'auki Biro da takarda yayi rubutu sannan ya fito, ya aje masa kan kujerar da yake zaune, sannan ya koma bedroom had'a kayanshi..
Kamal ya d'auki tardar ya bude, ga abinda ke cikinta...
ASSALAMU ALAIKUM
Da farko dai maganar da zan fara yimaka itace kamal kaji tsoro Allah, akoda yaushe ka sani duniyar nan ba madauwama bace, kamal ka natsu ka komama Allah tun kafin yayi fushi da kai, ni yanzu ansa sunana zuwa Maiduguri bansani bah koh Allah zai sake had'amu, sannan kuma wallahi yanzu duk laifin da kayi min nayafe maka sai dai kuma ka ruk'i Allah ya yafimaka, dan Allah ko bayan ba raina kar kayi ma Muhabbat!!! Komai indai bah taimakonta za kayi bah, kuma dan Allah ka kulla da iyayena, sannan uwa uba kamal ka kula da sallah .... Na barka lafiya daga dan uwanka Hameed Abubakar.......
" Allah sarki sanda kamal ke karanta takardan nan hawaye ya fara fita daga idonshi saboda maganan da yaji Hameed yayi mashi, zuciyarshi ta karaya, Mek'ewa yayi ya nufi bedroom, koh da shigarsa yasamu Hameed har ya d'auki jakarshi, kamal ya fad'a jikin Hameed, ya fashe da kuka yace, "Hameed dan Allah kayi hakuri da abinda ya faru kuma I promise u from today, duk wani abu da nake na daina insha Allah kuma yanda katafi lafiya haka zaka dawo lafiya. " is OK kamal ya isah haka kamal na yafe maka inaso yanzu ka taya ni da addu'a, sannan dan Allah kar kayi ma Muhabbat dina komai. "Humm Hameed kenan wallahi bazanyi mata komai bah yanda ka barta haka zaka dawo ka sameta Lafiya. " yauwa my friend thank u very much, mutafi ka sauki ni a office because nasan yanzu mutanen na jirana.....
Allah sarki ni kaina sai da hawaye ya zoboman na tafiyar Hameed Maiduguri
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment