[5/21,7:00.PM] BY Fatima
MATAR MUTUM
146_150
NA
MRS UMAR
"Sai yanzu Abba yayi magana yace " gaskiya ne kamal nima na yanki wannan shawarar akan ka cika ma abokinka burinshi na auren Muhabbat don Allah in bazaka damubah. "Kamal shru yayi yana tunani maganarsu dady. "Ya za'ayi na aure Muhabbat bayan na so na cutar da rayuwarta ai nasan Muhabbat! kanta bazata yarda bah, saboda nasan yanzu Muhabbat ta tsneni sosai. " kamal ya kayi shru muna magana? "na'am dady toh dady zanyi tunani a kan magana. " kamal listen to me! ya kamata kayi tunani mai kyau wai....badon komai bah mukace ka aure Muhabbat bah sai dan cheto, yarinyar d'aga cikin halin da take. "Toh shkenn dady ba damuwa na aminci Allah yamabu sa'a but ina tunani Muhabbat bazata aminci bah, dana zama mijinta!!!!! " da sauri mom tace "haba kamal ai nasan Muhabbat zatayi murna da wannan maganar. " Haka ne saratu in anjima zanje nasamu mahaifinka sai muje ayiwa mahaifin Muhabbat din magana, dan haka tashi kashiga dakin dan uwanka kaje ka huta, Allah yayi maka albarka. "Amin dady.
" Kamal ya tashi yashiga bedroom din Hameed kan kujera ya zauna yana tunani yanzu tayaya zai aure Muhabbat alhalin babu soyayya a tskanunsu yasan ko ya auren Muhabbat bazata tabba sonshi bah saboda abinda yayi mata, yace "a gaskiya ada na cuci rayuwata, gashi Muhabbat macece da kowani namiji zai sota, kai bama wannan bah yanzu su dady da suke cewa na aure Muhabbat idan Hameed bai mutuba fa inyazo da wani ido zan ganshi kai this is impossible. " kamal ya buga hannunsa saman kujera dai dai lokacin da yagama maganarsa a zuciyarsa, Minal ce ta turo k'ofar dakin ahankali, da sauri ya d'aga kai ya kalli Minal, ta saba da tashigo ta fada jikin Hameed, toh yau ma haka ta shigo da gudu ta fad'a jikin kamal.....
"Ji yayi tskar jikinshi tatashi wani yar!!!! Ahankali yace " Minal miye haka? "Toh Yaya kamal oyoyo nazo nayi maka. " hummm Minal haka ake oyoyo sai anfada jikin mutum. "Oh sorry ya kamal wallahi nasaba da yi wa ya Hameed. " da sauri Minal ta bata fuska kamar zatayi kuka tace "ya kamal wai da gaske ya Hameed ya rasu? " tanayin tambayar dai dai lokacin da hawayen da ke idonta ya sauka, da sauri kamal ya d'ago kanshi yana kallonta cikin murya kasa kasa yace "waya gaya maki? " humm ya kamal kar kayi man karya ai mom ta gaya man komai. "Minal bamu da tabbas Hameed ya mutu saboda cikin wanda akaga gawarsu bata Hameed aciki, dan haka ki daina kuka. " kamal yasa hannunsa yana goge ma Minal hawayen idonta...
Haka suka dinga fira da ita tana bashi dariya!
BAYAN SATI DAYA
Bafulatanin da ya d'auki Hameed yanayi mashi magani , hankalinshi ya tashi sosai saboda yau sati Hameed d'aya a kwanci tunda aka kawoshi koda dan yatsanshi baiyi motsibah. "Matar da ke gidan yaduba yace " fadima kina ganin wannan yaron tana da rai kuwa? "Baffa tana da rai da yardar Allah. " yanzu me zamu bata tatashi? Yauwa d'auko man magani nan a bata. "Toh baffa. " fadima tatashi, tashi ga dan dakisu ta d'auko magani ta kawowa baffa! Ya amsa ya d'aga kan Hameed yana bashi, fadima tace "baffa kasan wani Abu wallahi baffa tunda yaron nan tazo gidan nan nake jinta a jikina kamar nasanta. " toh ai dama hakane fadima akwai wanda zakaji kana sonshi a rayuwarka. "Yana gama maganar ya kwantar da Hameed, sauka tashi zasu fita, ai kam hameed yafara nishi da sauri fadima ta dawo, nan fa baffa ya farayi mashi addu'a, can sai ya fara ajiyar zuciya yana bud'e idanuwanshi a hankali ai kam yana budewa wanda ya fara had'a ido ta ita sai fadima da sauri ya bud'e baki yana nunata da danyatsanshi yace " ma!!!!!!!!!!!!
Toh masu karatu wai Dan Allah wacce mata ce wannan? tsaya muga suwa ke da Basira cikin masu karatu...
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment