Wednesday, 13 July 2016

MATAR MUTUM 171_175

[5/30,8:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
.

171_175

NA
MRS UMAR


Washe gari Hameed tunda ya tashi ya tafe, masallaci sallah asuba bai dawo bah, sai da gari ya fara haski, kafin ya dawo Muhabbat har ta tashi tayi sallah asuba, kitchen ta nufa danyi masu kayan breakfast, tana zuwa kitchen din ta rasa yanda zatayi saboda gas ta gani gashi bata iya kunawa bah, tana nan tsaye tana tunanin yanda zatayi sai ga Hameed yashigo, ta baya ya rungometa yace "my wife kin tashi lafiya " lafiya Qlau. "Hameed yajuyo da ita gabansa yana kallonta yace " me zakiyi haka? "Hmmm dama..... " dama me? kinga je kiyi wanka yanzu ki shirya zamuje gidanmu yanzu kinji koh? "Kai ta d'aga masa alamar eh, tajuya ta tafe, binta yayi da kallo, tana zuwa tashga toilet danyi wanka, shikuma ruwan tea yasa a wuta, bata dade bah, ta fito d'aga wankan, wajen mirror ta nufa ta zauna yin kwalliya duk da ba kwalliyar ta iya bah, amma tayi kyau masha Allah, bayan yagama yazo ya kirata suka zauna karyawa, kunya duk ta kamata, haka suka gama sannan shima ya tashi yashiga toilet dan yin wanka, ita kuma tana nan zaune kan kujera, yana gama wanka yafito dagashi sai towel, da sauri Muhabbat ta kauda kanta dan kaunya, murmushi yayi ya nufa inda kayansa yake ya saka, saida yagama sannan yace " tashi mutafe. "Hannunta ya kama yasa mata hijabi, suka fito yace wa mai gadi ya rufe gidan, suka shiga mota Hameed yana driven amma hannunsa yana kan kafadar Muhabbat,ahaka har suka isa suna zuwa suka samu har kamal sun iso shida Minal, Muhabbat suna yin sallama kasa shiga tayi saboda gani fadima da tagani zaune, a zuciyarta take fad'a Allah mai iko kuji wata Mata kamar mamana. " Ashe duk magana nan a waje take yinta,fadima tace "Muhabbat nice fah mamanki. "Allah sarki uwa mai dad'i, da gudu Muhabbat ta fad'a jikin fadima ta mantama akwai, mutane a daki, nan ta fara kuka tana fad'in cewa " mama dama kina nan amma kika tafi kika barni har tsawo wannan lokacin. "Muhabbat kiyi hakuri wallahi Nima ba yanda naiya, saboda dana zauna a gidan nan toh wallahi yanzu da babu ni a duniya. " toh mama amma ya akayi kika San nan gidan? "Humm sa nadiyar Hameed nasan nan gidan Muhabbat. "Ban gane bah. " fadima tabah Muhabbat labari duk abinda ya faru, sai yanzu mom tayi magana, tace "toh Muhabbat abarta haka azo mugaisa koh, kunya ce duk ta kamata..

Nan fah Hameed yace " ya kamats kutaso muje gidansu Muhabbat. "Mom tace " gaskiya ne Hameed. "Dakyar suka samu fadima ta yarda, saboda cewa tayi ita ba inda zata, dukka gidan suka fito har da Minal da kamal, suka shiga motocinsu, gidan suka nufa direct, ai kam suna zuwa Muhabbat akace ta fara yin gabah tana shiga tasamu Innah da Lami, Innah tace " toh munafika ya koroki koh? "Hameed ya amsa yana dai dai shigowa yace " ai ni nafi karfin nakori Muhabbat, ai auranmu mutu ka raba takalmin kaza. "Toh marar kunya dama baka mutu bah. "Maganar Innah tatsaya ne a lokacin da fadima ta shigo, ido tazaro tana nuna ta da danyatsa. "Hameed yayi murmushi yace " ban mutu bah, dama kinaso namutu ne? Toh Allah bai baki sa'a bah. "Ashe Abba yana tsaye, ai kam yana gani fadima kanshi ya dafe, saboda abinda yasokeshi, Innah tace " Lami kinga ya dawo itama wannan shegiyar ta dawo "hhhhhhhhh ai dole nakuma wajen bako hhhhhhh ai gidan nan nawa ne ni d'aya hhhhhhh. " dukka mutane wajen bin Innah sukayi da kallo, saboda da alama Innah ta haukaci, ai kam ta haukaci da gudu tafita tana dariya tana wayyo, Lami kuwa ai bah magana, sai yanzu suka lura da halin da Abba yake ciki, ai kam nan suka kamasa...

Ya dan d'auki lokaci kafin yafara magana, yace "fadima yau kece a gabana me yafaru dani har na manta dake, dan Allah ki yafeman. " malam na yafi maka. "Nan fa suka tashi gaba d'ayansu suka koma gidansu Hameed, bayan sun koma Hameed yace wa Muhabbat tatashi su tafi gida, mom tace " ba inda zata inaso su danyi kwana biyu ita da Minal akwai abinda zamu dan nuna masu. "Hameed yace " mom wane Abu ni gaskiya kubani matata mu tafi gida. "Toh marrar kunya, kamal ma bai magana bah sai kai. " dady yace " a'a saratu ba'a haka ki basu matansu sutafi gidan. "A'a Alhaji wallahi akwai abinda zan nuna masu. " toh shkenn, toh kuyi hakuri har ta gama, nasan dai irin abin nan nasu na mata zata basu. "Mom ta bata fuska tace " kajika koh Alhaji da wata magana gaban yara. "Toh ai gaskiya na fad'a, yauwa Hameed ya kamata, Muhabbat kasata makaranta. " eh dama dady na yanke shawarar zan sata school dinsu Minal sai sudinga zuwa tare. "Yauwa ai kayi shawara mai kyau..

Nan fah su Hameed sukace suma ba inda zasu, sai dai ya zauna dakinshi, mom tace bata yarda bah, dad yace a'a su zauna ba damuwa.....


®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment