Wednesday, 13 July 2016

MATAR MUTUM _151_155

[5/23,2:00.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM

.
151_155

NA
MRS UMAR




Hameed ya bud'e baki yace " Muhabbat!!!!!!!!!! "Da sauri fadima ta d'aga kai ta kalleshi cikin firgita, tace " Muhabbat kuma yaro kai dan Nigeria ne dama? Muhabbat d'ina nada rai bata mutu bah? Yaro kiyi hakuri kiyi man bayani don Allah. "Hameed ajiyar zuciya yayi mai k'arfi sannan ya numshi idonshi, sai da ya d'auki wani lokaci kafin ya bud'e idonsa, sannan ya d'aga mata kanshi alamar eh. " yanzu dama Muhabbat na duniya mairo bata kashe tabah? shi kuma malam koya biyo sawona, toh amma ya akai ni ban sankaba bayan ni duk zamana a garin Katsina bansan malam nada yan Uwa masu kudi bah! kuma gaka da alama kai soja ne. "Eh ni soja ne kuma ni ba Dan uwansu Muhabbat bane ni mijin da zan aure tane insha Allah, mama dama kece mahaifiyar Muhabbat? " eh yaro nice. "Mama meyasa baki d'auki diyarki kun tafi tare bah, meyasa duk tsyon lokacin nan baki koma bah? ." humm yaro maganar mai tsayoce zanyi maka bayani in kasamu sauki, Allah yabaka lafiya ameen. " duk wannan magana da suke baffa na tsaye yana jinsu...

***********

Washe gari

"Dady yashrya ya tafi gidan mahaifin kamal, bayan sun gaisa dady yayi mashi bayanin abinda ya kawoshi, mahaifin kamal yayi murna da jin magana yace Allah yasa haka shine mafi alkairi ameen, dady yace "toh muwuce gidansu Muhabbat tare don suyi wa Abba bayani, gaba d'ayansu suka tashi suka fito mota suka shiga sai gidansu Muhabbat,
Yauma sunyi sa'a Abba baitafi kasuwa bah, Abba yayi murna da ganunsu sosai nan fa suka gaisa kafin dady yagabatar da abinda yakawosu, Abba yace " toh ai ni Alhaji banida wata magana duk abinda kukace ai yayi bah Matsala. "Dady yace " toh shkenn dama bikin yanzu yanda aka sashi saura sati d'aya, toh haka za'a barshi baza'a d'aga bah, dama Allah yayi kamal shine mijin Muhabbat, dama hausawa sunce MATAR MUTUM kabarinsa. "haka ne Alhaji. "Toh yanzu idan kashiga kayiwa ita Muhabbat din bayanin. " toh mungode. "haka su dady sukayi masa sallama suktaafi gida abinsu,shi kuma gida yashiga yasamu Inna yafara gaya mata abinda yafaru Muhabbat na gefinsu zaune, Abba yana gayawa Inna zufa na sauka a jikinta, yayin da Muhabbat hankalinta ya tashi sosai sai hawaye ke bin idonta, Abba yana gama magana yajuya ya fita, ai kam Inna tamike tsaye tana fad'in. " kutt ni za'ayiwa iskanci au ba'a rabu da bukar bah an yayi garba an haihe Abu kenn ta nan zasu billo, toh wallahi banga ta zama bah. "muhabbat itako a cikin zuciyarta take cewa. " ta Yaya zan aure dan iska nidai wallahi bana sonka bana sonka Allah sarki ya Hameed dina.......


****************

a kwana a tashi ba wuya wajen Allah, yau saura kwana uku Muhabbat ta zama Amaryar kamal za'a Daura masu aure ranar asabar da misalin 2:30PM, yayin da Inna hankalinta ya tashi sosai ta rasa zaune ta rasa tsaye, haka ma Muhabbat kwatata bata son auren, ango kuwa ai ba'a cewa komai wajen murna su Minal sune k'awayen Amarya......


*****
Jikin Hameed yayi sauki sosai saboda yanzu yana tafiya ko ina, hakan yasa sukayi magana da mahaifiyar Muhabbat tare zasu koma da ita Nigeria amma yasha wahala kafin yashawo kanta ta yarda zata bishi badan komai ta yarda bah sai saboda diyarta, sun aji rana zasu tashi ranar jama'at sai su isa ranar asabar tunda mota zasu hau ba jirgi bah, hameed yace wa fadima. "Toh Allah ya kaimu ranar amma inaji a zuciyata kamar wani Abu zai faru kafin ranar. " baffa yace "haba ka kwantar da hankalinka ba abinda zai faru insha Allah. " toh shkenn na yarda Allah ya kaimu ranar. "Amin......


Toh masu karatu da alama fah! sanda Hameed zasu iso garin Katsina sannan Muhabbat ta zama Amarya kamal,

Mudaije zuwa......

®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment