[5/16,7:15.PM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
136_140
NA
MRS UMAR
Allah sarki kamal duk ya damu kamar anyi mashi mutuwa, saboda rashin abokinshi kosa dashi, kamal ya natsu, ya daina duk abonda yake, zaune yake kan sallaya, yana lazimi hawaye sai fita yake a idonsa, abin tambayar bansan kukan da yake bah,ko kukan me yake oho sanin gaibo sai Allah,
afilin kuwa abinda yake fad'i cewa yake. "gaskiya dole naji na samu Muhabbat na bata hakuri kan abinda ya faru, gaskiya ban kyauta bah, Ashe ada ina chutar rayuwata, duk abinda Hameed ke gayaman gaskiya ne, Allah sarki abokina naso ace kana kosa dani na gyara halina. " sai kawai ya fashe da kuka,sai da yaci kukanshi ya gaji kafin yatashi yayi Shiri zuwa office....
Itama Muhabbat duk ta damu da rashi masoyinta,saboda duk ta rami dama abinku da fulani da k'aramen jiki, Inna tana jin dadi ganinta haka, gashi kwana biyu bataji islamiyya bah, ballatana taji d'aga bakin Minal ko suna waya da Hameed, haka ta d'auki talla ta tafi badan ranta nasobah, amma koda yaushe da tunanin Hameed take kwana take tashi...
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah yau watan Hameed d'aya da sati biyu kenn, a Maiduguri, sai dai kash!!! Tunda Hameed ya tafi ba labari, hankalin mom ya tashi sosai hakama dady saboda rabunsu da suji muryar Hameed tun ranar da ya kirasu yace "gashi ya isa garin Maiduguri. " mom ne da dady zaune a falo suna magana mom tace. "A gaskiya Alhaji ya kamata musan halin da yaron nan yake Alhaji hankalina ya tashi, gashi bikin nan yau saura sati biyu, Alhaji ya zamuyi yanzu. "Haba saratu kidaina kuka mana kinaso hankalina ya tashi, haba saratu da wani zanji? Ki kwantar da hankalinki insha Allah ba abinda ya faru da Hameed, yanzu zan kira kamal inji d'aga bakinshi. " yauwa Alhaji Dan Allah ka kirashi muji abinda ya faru da Hameed dina...
Dady wayarshi ya d'auka ya danna ya kira kamal, cikin girmamawa kamal ya d'auki waya ya gaishi da dady, dady ya amsa bayan dady ya amsa sai yayi shru jim kadan yayi ajiyar zuciya yace "kamal inaso ka gaya man me yafaru da abokinka in'na kira numbershi baya zuwa. " Allah sarki dady maybe nan Katsina kuna da Matsala network amma ko yau manyi waya dashi yananan lafiya Qlau. "hummm kamal kenn nifa ba yaro bane Dan Allah ka fitu fili ka gaya man, gaskiya nifa musulmi ne na yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau wallahi duk abinda ya faru da Hameed na yarda da kaddara zanyi mashi addu'a." Allah sarki kamal kuka ya fashi dashi kamar karamin yaro yace, "gaskiya ne dady bama waya da Hameed tun ranar da ya isa gari Maiduguri rabamu da waya, naje office nayi binciki sai dai dady yanda rahoto ya nuna man cewa, inda su Hameed suke ankai masu hari bomp ya tashi a wajen. "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN shkenn Hameed Allah yaji kanka. " wata uwar kara mom ta fasa tace Alhaji Hameed din ne yarasu wallahi karya ne Hameed dina bai mutu bah saboda naji a jikina Hameed yana duniya, insha Allahu sai naga yayan Hameed a duniyar nan. "Haba saratu ya kike irin wannan maganar karki manta kifa musulmace ki yarda da kaddara mana. " toh Alhaji yanzu shkenn alkawarin da ya daukarwa Muhabbat ba rabon ya cikashi, Allah sarki Muhabbat na tausaya maki Inama ace inda wani d'an da sai ya aureki!!!!!!!?
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment