[5/25,4:30.PM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
.
156_160
NA
MRS UMAR
Yau ta kama ranar Friday Hameed da fadima zasu kama hanyar dawowa Nigeria, inda baffa ya rakosu har tasha suka shiga motar fita dasu Maiduguri, kafin insunje suhau motar garin Katsina, fadima ta danyi kukan rabuwa da baffa, sannan Hameed yayiwa baffa godiya sosai...
Innah ce zaune a gaban boka ita da Lami sai faman kuka take masa wai yataimaketa kada yabari ayi auren nan, boka budar bakinshi yace "mairo abinda zan gaya maki kadaki yarda ayi auren nan saboda idan har kika bari akayi auren nan toh duk wani asiri da kikayi ya tashi aikin daga ranar duk wani farin cikinki zai kare. " haba boka yanzu ba abinda zakayi akai? "Hhhhhhh akwai mairo, mu har ance bamuda abinda zamuyi ai muke da abinyi, ga wannan idan kinje gida ki binne shi k'ofar gida, ina gaya maki da kinyi wannan anyi angama, amma kada ki bari wani ya ganki, da wani yaganki toh aikin yakare sai tayi aure. " Toh shkenn boka mungode,
Su Innah aka fito daga wajen boka ana murna..
Su Minal k'awayen Amarya sai kaiwa da kawowa, zaune take a gaban Muhabbat tanata fama da ita tazo suje a gyara mata jiki saboda gata Amarya ai bata zauna haka bah, budar bakinta tace "ni ba idan zani kwalliyar me zanyi bayan Wanda zai ganta baya duniyar yanzu. "Haba Anty Muhabbat miyasa kike fad'a haka ai da ya Hameed da ya kamal ai duk d'aya ne. "Humm minal kenn bazaki taba ganewa bah. " eh nidai naji muje koda salon ne ayi maki saboda wallahi mom tace nazo mutafi tare dake, konaje nacewa mom kince bazakibah? "Haba dai wace ni, badamuwa bari Innah tadawo sai muje nasan yanzu takusan dawowa. " Muhabbat narufi baki sai ga Innah ta danno kai, Minal ta gaida ita kafi Muhabbat tace masu zasu fita, Innah tace ai badamuwa, saboda taji dadin rufe maganinta.....
Waje suka fito suna fita Muhabbat taga Ashe da mota ma Minal tazo, jikin motar suka nufa Minal ta bud'ewa Muhabbat tashiga gaba, tana shiga taga mutum zaune amma ya kifa kanshi a stery motar ita dai tashiga ta zauna sannan Minal ta zauna a baya saida suka rufe k'ofar motar kafin ya daga kanshi, kirjin Muhabbat ne yabuga saboda ganin fuskar kamal a gabanta nandanan zufa yafara binta shikam key yasa ya tada motar, suka fara tafiya Muhabbat jitake kamar tayi tsale ta fita motar sai da sukayi nisa ba Wanda yayi magana kafin yace "Minal ina zakuje salon din? " tace "a ZAINAB SALON zamuje tafi iyawa. "OK is gud kefa madam baki iya gaisuwa bah kin shgo ba gaisuwa. "Muhabbat tayi shru bata tankashi bah, kai ya girgiza yayi murmushi no problem tmrw u will be my wife, yayi parking dai dai lokacin sun isa zainab salon, suka shiga ita da Minal da yake shagon maza basa shiga sai mata kawai, suna zuwa ba mutane kuwa aka fara masu...
RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA
yau takama ranar asabar wato ranar da za'a daura auren KAMAL DA MUHABBAT da misalin 2:30PM yanzu kuma wajen misalin 11:00.AM kenn Amarya sai faman kuka take Innah kuwa ai takoma kamar mahaukaciya...
Mutane tafiya su Hameed tafiya tayi nisa yanzu haka suna cikin garin Zaria saidai kash!!!!! Motarsu tasamu Matsala a hanya suna ta fanan gyara...
GARIN KATSINA
jama'a yan daurin aure ancika k'ofar gidan su dady da yake Abba yace ba Matsala kawai a daura gidansu dady ba wata Matsala shyasa duk Wanda yataho gidansu Hameed suke nufa, wayaga ango sai faman bud'e baki ake, nidai cikin gida nashiga nasamu wajen na zauna ina kallon jama'a d'aya bayan d'aya, wata tsohowa tace " Allah sarki ba rabon ayi auren nan da Hameed, Allah yace wannan yarinyar matar kamal ce dama ance MATAR MUTUM kabarinsa. "Eh wallahi baaba. " mom ce ta amsata, daga waje muka jiyo muryar mutane suna cewa fatiha an daura,ana cewa an daura mom ta fashi da kuka tace "shkenn yau Muhabbat ta zama matar kamal, Allah sarki Hameed!!!! Maganarta ta tsaya ne a lokacin da akayi sallama gaba d'aya mutanin dakin suka juya....
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment