Wednesday, 13 July 2016

MATAR MUTUM 141_145

[5/19,12:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM


141_145

NA
MRS UMAR


Saratu karki damu indai wannan ne, ai ga kamal nan na tabbata kamal zai cikama abokinshi burinshi. "Shkenn Allah yajikanka Hameed. " suna cikin kuka haka kamal yasake kiran dady da sauri dady ya d'auka. "Ina jinka kamal ya yake cikin? "Toh dady yanzu dai gani a office commander yace man missing in action, so ba'a ganshi ba. " oh my God yanzu kenn bama a ga gawarshi bah? "Eh dady addu'a kawai ya kamata mutaya Hameed da ita. " toh shkenn kamal mungode. "Toh dady gobe insha Allah zan kama hanya nazo muyi magana. " toh Allah yakaimu. "Amin. "Haka kamal ya kashe wayarshi, dady yace bari yaje yasamu mahaifin Muhabbat ya gaya mashi abinda ya faru, haka yafita tafiya gidansu Muhabbat....

Dady gidansu Muhabbat ya isa yana zuwa yayi sa'a Abba zai tafi kasuwa, sai da suka gaisa kafin dady yayi mashi bayanin abinda ya kawoshi, duk abin Abba saida yaji ba dadi, gida yashiga yana zuwa ya gayawa Inna abinda yafaru, Muhabbat inda take hawaye ya fara fita d'aga idonta, sai da Abba ya juya yafita, kafin Innah ta kece da dariya harda ihu tace " Wanda baiji bariba yaji ohoho yau dunuya tayi man dadi abinda nad'e ina jira yasamu yau Hameed yazama gawa. "da sauri Muhabbat ta d'ago kai tana kallon Innah, saboda abin mamaki yake bata. " kardai ace Innah ita ta kashe Ya Hameed nashiga uku shkenn ya Hameed ya barni dama shi yayi niyar taimakona. "Muhabbat duk acikin zuciyarta take magana, dadai taga kuka bazayi mata komai bah buta ta d'auka tayi alwala tayi sallah....

GARIN MAIDUGURI

kwanci yake bai san inda kanshi yake bah cikin dajine sosai ba mutane ko alama sai kukan tsentsaye sai iskan sararin sama niya, ana cikin haka sai ga wani bafulatani zai wuce, ya ganshi kwanci a kasa da sauri bafulatanin nan yadawo, abinku da Fulani da tausaye, da sauri ya d'aukeshi ya sashi cikin keken shanu, da alama shi ba Fulani Nigeria bane Fulani Cameron ne, aikam hanyar boda ya nufa direct yak'etara bodar Cameron wani kauye ya nufa dashi mai suna bonheri kauyen dukka fulanine, yana zuwa wata kyakkyawar mata tazo ta tareshi matar atatarta bazata wuce shekara 40 bah, matar masha Allah, a cikin harshen fulatanci tayi mashi magana. "Baffa jab'ama. " yauwa FADIMA...
A'a baffa bak'omu kayi gidan? "Wallahi fadima kingashi a dauwa dauketa gata nan kamar ta mutu bah rai, amma bari yanzu zan mata magani zata tashi da yardar Allah....

GARIN KATSINA

Yau kamal ya iso garin KT lafiya, amma da kaganshi kasan yana cikin damuwa, bai nufa gidansu bah, gidansu Hameed ya nufa direct, yana zuwa ya samesu zaune a falo, akam yana yin sallama mom ta fashe da kuka, da sauri yakarasa wajen mom ya duka shima kukan ya fasa, mom tace " kamal kaga yanda Allah yayi damu , kamal Ashe ba rabon naga auren Hameed, alkawarin da ya dauka ba rabon ya cikashi. "Mom don Allah ki daina kuka insha Allah komai zaizo da sauki. " toh shkenn kamal amma inaso yanzu ka daukarman wani alkawarin. "Toh mom insha Allah kowane alkawarin ne zan maki. " toh kamal dama ba komai bani illa inaso alkawarin da abokinka ya d'auka zai aure Muhabbat tunda yanzu baya duniyar inaso yanzu kamal ka ainshaure Muhabbat!!!!!!! "Da sauri kamal ya zaro ido yace mom ai wannan bazai..... " dakata kamal kace kayi man alkawarin, dan haka yanzu magana ta wuce insha Allahu lokacin bikin da akasa baza'a daga bah.......


®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment