Wednesday, 13 July 2016

MATAR MUTUM 166_170

[5/29,12:00.PM]BY FATIMA

MATAR MUTUM

.
166_170

NA
NRS UMAR


"Ahankali ta numshe idonta saboda yanda yake shafa mata gashin kanta, cikin murya kasa kasa yace " nasan kinyi missing dina koh? "Kai ta d'aga alamar eh. " yace "good my wife ai nasan kina sona. " kamal gani yayi idan ya tsaya jiransu toh zai kwana a haka, sai kawai ya dake yace "toh malam, ai Luv din ya isa haka, ko kunyata ma bakwaje, toh nima bari na tafi wajen Amaryarta. " au! Sorry fah na manta kana dakin, toh zoka zauna muyi magana. "A'a haba wani zama, ai sai kudasa man hawan jini. " Hameed yayi dariya warda sai da ta baiyana hak'oransa, ahankali kamal yazo gaban Muhabbat ya fad'i kasa sai hawaye ya fara bin fuskarshi yace "Muhabbat bansan da wani idon zan kallekibah, Muhabbat dan Allah kiyi hakuri abinda yafaru a baya, SON ZUCIYA yaso yakaine ga halaka, Muhabbat wallahi yanzu NAYI NADAMA sosai, kiyafini. " Muhabbat tayi shru bata bashi amsa bah, ahankali Hameed ya juyo da fuskarta yana kallonta, yace "please matata kiyi hakuri ki yafe masa wallahi na tabbata kamal yanatsu yanzu. " toh bah damuwa na yafe masa amma yaci albarkacinka. "Yauwa my wife, yanzu dai Allah ya amsa addu'armu yau kin zama matata shikuma kamal Minal ta zama matarshi........ " eh Yaya, ta Yaya Minal ta zama matar kamal? "Yanzu zakiji yanda akai Minal ta zama matar kamal. " nan fa Hameed duk yabata labarin yanda akai, sai dai bai gaya mata tare suka taho da mamanta bah, saboda yanaso da safe sai ya kaita, Muhabbat ta girgiza kai tace "Allah mai iko ba. " nan fa suka sha fira da kamal, ya danyi mata nasiha, hafin Hameed ya rakosa har wajen motarsa, bayan ya tafi Hameed ya dawo cikin gida, ai kam inda yabar Muhabbat zaune nan ya samita, toilet ya nufa yayi alwala sannan yafito, wardrobe ya bud'e ya dauko mata wasu kayan bacci ya bata, yace ta shiga toilet tayi wanka sannan tayi alwala tazo suyi sallah, kayan ta amsa ta nufa toilet, shikuma kayan jikinshi ya cire ya saka jallabiya, kan kujera yakoma ya zauna yana jiran ta fito, bayan ta gama wankan tasa kayan da yabata, Muhabbat bin jikinta tayi da kallo, saboda yanda kayan sukayi mata sunyi mata bala'in kyau duk wata surar jikinta kana kallonta, Hameed gani yayi bata da niyar fitowa sai kawai yatashi ya nufa toilet din ya bud'e k'ofar, yana budewa ya ganta tsye a toilet din tana wasa da yan yatsita, murmushi yayi ya numshe idonsa ya nufa inda take, yakama hannunta ya fito da ita, hijabinta ya dauka yasa mata, sannan ya kabbara sallah, bayan sun gama Hameed ya zauna yana masu addu'a, yadade yana addu'a har bacci yakwashe Muhabbat, juyowa yayi yaga har tayi bacci, yayi murmushi, ya dauketa cak sai saman gado ya kwantar da ita, shikuma yacire jallabiyar jikinshi ya hau kan gado, yajanyota jikinshi yafara shafata da sauri tabude idonta, nan fa jikinta ya fara rawa, shiko ci gaba yayi da shafata, can yakai hannunsa a kan dukiyar Fulani, kuka Muhabbat ta fasa jikinta narawa, can sai ga wayarsa tayi k'ara juyawa yayi ya dauka amma, bai tsaya yaga waya kirasa bah, janyo Muhabbat yayi saman k'irjinsa yana wasa da gashin kanta, bayan ya dauka yaji muryar tace "Hameed dama na manta ince maka dan Allah kabar yarinyar nan karkayi mata komai, kana jina? " eh mom. Bayan mom ta kashe wayarta Hameed yace wa Muhabbat "don't worry ki kwanta kiyi bacci bah abinda zanyi maki kinji koh....

Su kamal ango yana zuwa gidansa yasamu Minal har tayi bacci murmushi yayi yanufa dakin saboda bayaso yatakora mata...

®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment