[5/26,7:00.PM] BY FATIMA
MATAR MUTUM
161_165
NA
MRS UMAR
"Da sauri mom ta mik'e tsaye muryarta na rawa tana nunashi da danyatsa tace " jama'a waye nake gani a gabana? Ko mafarki nake idanuwana nanuna man ga Hameed a gabana. "Jama'ar dakin gaba d'aya suka had'a baki sukace muma abinda muke gani kenn, yanzu dama Hameed bai mutu bah kenn. " ahankali hameed yak'araso inda mom take ya kama hannuta ya zaunar daita yace, "mom inanan da raina BAN MUTU BAH Allah yasa da sauran kwanana a gaba. "Yanzu dama hameed kana duniyar nan duk tsayon kwanakin nan? Sai kawai mom da fashi da kuka tana fad'in. " shkenn Hameed kazo a makare kazo a lokacin da Muhabbat ta zama matar kamal dama Allah yayi Muhabbat bah matarka bace. "Oh my God mom please stop crying, mom kidaina kuka ko yanzu banzo a makare bah saboda Allah yariga ya rubuta MUHABBAT MATATA CE. " what, ta yaya Muhabbat ta zama matarka bayan angama daurin aure? "Hameed yayi ajiyar zuciya sannan ya gyara zama yace " mom muna cikin garin Zaria motarmu ta samu Marsala wajen 11AM tunda muka taso a Cameron kirjina ke bugawa har lokacin da motarmu tasamu Matsala da naga motar bata da niyar gyaruwa sai muka sake mota, misalin 2:PM muka shgo nan cikin garin Katsina,wata mota muka samu Wanda zai kawomu har nan k'ofar gidan, abin mamaki ina zuwa sai nagan taron jama'a da sauri na k'arasa wajensu, hummm jama'ar wajen sun tsorata da ganina, bayan sun gano da gaske nine ban mutu bah sai mahaifin kamal yace tunda na dawo bai kamata adaura da kamal bah,kawai a daura auren dani, shi kuma dady hakan yasa yace toh bai kamata kamal ya tashi haka bah kawai ya bashi auran MINAL!!! Sai kawai aka had'a aka daura auren yanzu minal itace matar kamal ni kuma Muhabbat itace matata. "Mutane dakin sukace Allah mai iko MATAR MUTUM kabarinsa Allah dai yace Muhabbat sai ta zama matarka. " mom ta fara share hawaye idonta tace "yanzu minal aka daura auenta da kamal, toh ina Minal zata iya zama gidan miji. " haba Muhabbat ma zata iya zama gidan miji ballanta Minal. "Toh marar kunya au kadawo. " dukka dakin akasa dariya, mom takai dubanta da fadima tace "au wai harda bakuwa kake tafe? da sauri hameed ya d'aga kai saboda ya manta ma suna tare yace " I'm sorry, mom wannan itace mahaifiyar Muhabbat tare muka tahu daga Cameron. "Nan Hameed duk ya basu labari abinda yafaru,mom tayi murna sosai da ganin fadima nan fa aka fara karramata....
Wayaga amare basu san abinda yake faruwa bah. Muhabbat sai faman kuka take tunda taga 3: yayi tasan an daura auren yau ta zama matar kamal, Minal Keta aikin bata hakuri amma taki hakura, wata kaurar Minal ce da tagaiyato mai suna FIDDAUSI SODANGI tace " haba Muhabbat ya kamata kidaina kukan nan haka ki godewa Allah, shi Allah da yasa kamal ya zama mijinki ai yasan abinda yakeyi, ki yarda da kaddara mana."Humm SODANGI bazaki gane bane, amma inaji a zuciyata kamal bazai taba zama mijina bah. "Tana rufe baki phone Minal yayi k'ara da sauri ta daga saboda ganin sunan dake kan screen din wayarta, dady ne yace " minal kiyi sauri kidawo gida yanzu ina nemanki. "Minal tace "toh dady ganinan zuwa, " tana fitowa gidan ta nufa direct, falon dady tayi tana zuwa ta sameshi zaune kan kujera, ta gaidashi sannan ya amsa yace "minal kin yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau? " ta d'aga kai tace "eh dady na yarda da ita saboda akoda yaushe a islamiyya ana gaya mana mu yarda da kadarra mai kyau ko marar kyau dan haka dady na yarda da ita. " yauwa Minal ai nasani, toh inaso ki bud'e kun'nanki kiji abinda zan gaya maki Minal!! D'aga yau kin zama matar aure..... "what?!!! Dady matar aure fa kace, ta yaya zan zama matar aure bayan ni bani da saurayi. " Minal karki manta kefa kikace man kin yarda da kadarra. "Eh dady na yarda da ita, toh Minal na daura maki aure da kamal ne saka makon hameed yadawo bai mutubah. " Dady Yaya Hameed yadawo bai mutu bah? "Eh. "Toh yana ina. " gani minal. "Da gudu Minal ta fad'a jikinshi tana " dama yaya kana da rai baka mutu bah duk tsayo lokacin nan. "Eh Minal, Please Minal promise me zaki rike kamal a matsayin mijinki. " Minal ta dago jikinta d'aga jikin Hameed tana share hawayenta tace "yes yaya I promise u zan zauna dashi a matsayin mijina, " yauwa my sweet sister....
Misalin karfe 8:PM dady ya aika da mota yace a d'auki Muhabbat akaita gidan Hameed da ke kwado, har yanzu maganar da ake Muhabbat bata san da Wanda aka daura masu aure bah, Allah sarki haka aka d'auki Muhabbat ba dan rakiya ko d'aya, saboda tun safe Innah bata gida har yanzu bata dawo bah, d'aga ita sai driver, haka ya nuna mata inda zata shiga ya nuna mata dakinta, tana zuwa ta fad'a kan gado tana kuka mai cin rai, sallamar kamal taji amma bata amsashi bah, saboda ta kifa kanta a kan gado, ahankali hameed ya zauna dai dai in da kanta yake cikin murya kasa kasa yace "haba uwar yaayana kukan me kike? " cikin zabura ta mike tsaye taga kamal tsaye sai ga Hameed zaune kan gado sai kawai ta fashe da kuka, tace "nashaga uku dan Allah Yaya Hameed kayi hakuri wallahi banida laifi wajen auren nan, ka koma ka kwanta wallahi nayi maka alkawarin bazan yarda dashi bah. " Hameed abin dariya ma ya bashi yace "oh my God", Muhabbat please come down, Muhabbat yau Hameed ne a gabanki ban mutu bah ina nan da raina. " Yaya Hameed da gaske Kaine baka mutu bah? "Eh nine. "Da gudu Muhabbat ta fad'a jikin Hameed tana kuka, hannunsa yasa ya dago kanta ya had'a kanshi da nata yana kallonta yana Shafa kanta ai kamal juya fuskasa yayi...........
®EXTREME HAUSA WRITER'S
NA MRS UMAR
No comments:
Post a Comment