Wednesday, 13 July 2016

MATAR MUTUM 176_180

[5/31,4:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM
.

176_180

NA
MRS UMAR

Nan fah Abba yayi magana yace "nima ya kamata na maida matata dakinta tunda bah sakinta nayi bah. " dady yace "gaskiya ne dole fadima ki koma dakinki saboda har yanzu malam mijinki ne. " mom ma ta bada goyan baya dari bisa dari! nan fa dady yasa driver yace yakaisu gida.... Minal tace wa Muhabbat tataso sutafi dakinta sukwanta, suna tashi Hameed ya Mike zai bisu, mom ta daka mai tsawa tace "toh marrar kunya ina zaka bisu, maza kaja abokinka kuma kutafi dakinku, mutum banza kawai, ko kunyarmu bakaji. "Duk dakin sukasa dariya Hameed ya fara sosar keya.

Bayan su Muhabbat sunshiga daki, Minal tace " Anty Muhabbat sai kikaji an daura mana aure da yaya kamal, wallahi har yanzu abin mamaki yake bani, zan iya zama da ya kamal kuwa a matsayin mijina? "Humm Minal kenn zaki iya mana, ai bah abin mamaki bane, dama chan Allah yace kamal shine mijinki, kinsan MATAR MUTUM kabarinsa. " haka ne Anty Muhabbat, toh Allah yabamu hakurin zama dasu. "Amin. " Hummm ni Matsalata d'aya ce wallahi ban iya soyayya bah. "Hhhhhhh Minal kenn da abin dariya ai gara make, saboda ko yaya kinfini wayewa. " ai a nan bah wata wayewa. "Dariya sukasa su dukka, sannan sukayi addu'a suka kwanta....

Washe gari
Tunda safe mom tatashi, dan zasu fita ita dasu Muhabbat, dakinsu tashiga, Muhabbat ta duk'a har kasa tagaida mom, mom ta amsa cikin fara'arta, sannan tace masu " maza kushrya zamu fita yanzu daku, sukace toh, Minal ta fara shiga wanka kafin, bayan ta fito Muhabbat tashiga, itama tashiga tayi wanka, bayan sun fito suka zauna kwalliya, kunga yanda sukayi kyau kuwa? Yanda kukasan yan biyu wallahi haka sukayi kyau, kayan da sukasa sun amshisu! Kamar dansu akayisu, wani dan mayafi Minal taba Muhabbat tace ta rufa, dakyal ta amsa saboda cewa tayi bazata iya fita dashibah, sai da tace mata "ai a mota zamu fita kuma har inda zamu driver zai saukemu. " sannan fah! Ta yarda, falo suka fito suna fitowa kamshin turarensu ya duke hancin Hameed da kamal da sauri suka juyo daga inda suke zaune kan kujera, kowane bin matarsa yayi da kallo, saida suka iso sannan suka gaidasu, da sauri suka amsa, mom tafito itama har tashrya, tace "yauwa har kun shrya kenn toh mutafi. "Da Hameed da kamal ai had'a baki sukayi sukace " ina zaku haka da wannan kwalliyar. "Mom tace " gidan uwaku zamu. "Hameed yace " toh wallahi mom kafarku ,kafarmu, abokina taso mubisu. "Mom tace " wallahi Hameed kafita daga idona. "Toh yanzu mom haka zaki fita dasu bah hijabi jikinsu? " mom tayi dariya tace toh sarkin kishi kamar mace, ai a mota zamu kuma yanzu zamu dawo. "Nidai gaskiya mom matata taje tasa hijabi. " kamal yace "au matarka kawai banda tawa, ai Nima taje tasa hijabi. " dady na dai dai fitowa yace "kuna da gaskiya yara suje susa hijabinsu. " Minal ta turo baki tatafi ta d'auko hijabi, suka fita, driver ya daukesu mom tace masa ya kaisu gidan kawarta HAJIYA BINTA watau unguwar kwado, canko driver ya nufa dasu direct....

Sunyi sa'a sun samu Hajiya binta tayi murna da ganinsu sosai, sannan suka gaisa, sannan mom ta gabatar da abinda ya kawosu, Hajiya binta tace "don't worry Kawata indai wannan ne zanyi masu gyaran jiki na gani na fad'a sannan akwai wasu maguguna da zan basu sannan Uwa uba zan dafa masu kaza, gyaran jikin zanyi masu na sati d'aya. " toh nagode Kawata. "Haba badamuwa, yanzu San fara masu gyaran jikin.

Haka ta gama masu suka kama hanyar gida, da suka dawo sunyi sa'a su Hameed basa gida sun fita, dakinsu suka nufa direct,

Bayan sun shga sunyi wanka sunyi sallah, sannan suka zauna fira, Minal tace " hummm wallahi d'azu naji haushe fah da akace muje musa hijabi. "Toh ya zakiyi aure kenn ai. " Hameed ya turo k'ofa yace "ina my wife dina har kun dawo. " llah Yaya a gabana. "Ke ni tsaranki ne ina magana kina saman baki, zan fasa maki baki Yanzu nan. " a'a kaga malam karka taba man mata. "Kamal ne yanzu yayi magana, da Muhabbat da Minal kansu, suka sa kasa,


®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment