Tuesday, 12 July 2016

MATAR MUTUM 116_120

[5/11,3:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM

.
116_120

NA
MRS UMAR

Bayan barin su dady gidansu Muhabbat,ai suna tafiya Inna ta d'auki mayafinta sai gidan baba Lami, ai kam tana zuwa ta bata labarin an kawo kud'in neman auren Muhabbat, Lami tace, "wannan shgen yaro kice sai da yakawo kud'in Neman auren wannan shgeyar yarinya." Hummm kedai kawai ki bari ai indai akayi wannan auren shkenn asirina ya gama tunuwa,gashi maganar wannan bokan ma shru ba wata magana gaskiya ne zan sake wani boka Wanda zai man aiki sha yanzu magani yanzu.
"Haba mairo me kike tauna na baka nazuba, ai karkiji komai ai aikin bakon nan nayi, ai wannan alkhawari danayi maki kenn wannan auren bazai taba zama gaskiya ba saida suyishi a mafarki dan ubansu." Toh shkenn Lami gashi yanzu dai ansa biki nan da wata biyu masu zuwa. "Humm ai kafin sannan ya manta da yana k'iyama. " dukkasu sukasa dariya nan sukaci gaba da hiransu ta rashin tsoron Allah.......

*****************
BAYAN KWANA BIYU

Allah sarki yau ne Hameed zai koma garin port Harcourt Minal duk ta damu sai hawaye take, tace "Yaya yanzu in katafi sai yaushe kuma zaka sake dawowa? "Ahankali Hameed ya zage zip din jakarshi sannan ya zauna kan gado dai_dai inda Minal ke zaune, yayi murmushi sannan yace " humm Minal dama haka kike sona? So dan haka ki kwanta da hankalinki ai bazan d'auki wani time bah,zan dawo kinsan ba'asa bikin nan da nisa bah, zandawo biki na d'auki Amaryarta. Yauwa karki manta ki dinga kulla man da matata kinji koh my sister?. "Toh Yaya naji Allah ya saukeka lafiya but Yaya don Allah ka dawo da wuri, so yanzu zaka biya kayi ma Muhabbat bankwana koh? " Ah!! abinda yazama dole, ai dole naje naga fuskar matata kafin na tafi, bari ma kiga na tashi naje. "Hameed ya mek'e ya d'auki key din motarshi ya fito falo yana zuwa yayi cin karo da dady, yace " toh ina zuwa koma? "Humm wallahi dady dama inaso nayi ma Muhabbat ban kwana kafin na wuce. " ok ai haka nada kyau sai kadawo....

"Hameed ya nufi gidansu Muhabbat yana zuwa ya tura yaro a kirata ba'a b'ata lokaciba sai gata tafito, tana zuwa Hameed ya bud'e mata k'ofar mota tayi tsye tak'i shga saida taga ya bata rai kafin ta bude ta shga, ta zauna. " yaya ina wuni? "Lafiya, yakk. " Muhabbat tayi shru bata amsa bah, Hameed ya juyo sosai yana kallonta sannan yace "dama Muhabbat abinda ya kawoni inaso na gaya maki yau zan koma Port Harcourt hutuna yak'are so insha Allah da lokacin biki yayi zandawo. "Allah sarki, take Muhabbat hawaye ya fara fita daga idonta ta kasa magana, Hameed yace " ya salam Muhabbat me yakawo kuka kuma? wallahi Muhabbat I promise u zandawo ki daina kuka matata. "Sai kawai ta kara fashewa da kuka sosai, kanta ya d'ago yana kallonta cikin murya kasa _kasa kamar mai jin bacci yace " Muhabbat bakya so na koma wajen aikin? toh shkenn idan bakya so zan hakura Na zauna. "Muhabbat ta girgiza kai hawaye yaci gaba da fitowa a idunuwanta. " toh gaya man kukan me kike? "Cikin shashekar kuka tace " yaya wallahi yanaji a jikina kamar in ka tafi bazaka dawo. "Haba Muhabbat ya kike irin wannan magana kamar baki da tawalkali? ai Muhabbat insha Allah sai naga yayana dani dake koh matata. "Muhabbat taji kunya ta rufi idonta, Hameed yace "so yanzu me kike da buk'ata? " bakomai ina maka addu'a Allah ya mai doka lafiya. "Sai kawai ta sake fashewa da kuka ta rike hannunshi tace " don Allah idan kaje karka manta dani in ka samu yan matan fatako. "Hameed dariya ta bashi yanda ta kira sunnan gari, yace " ina, ai ba zan manta dake bah ai ke TAWA CE Muhabbat so kiyi hakuri yanzu zan wuce kar nayi missing jirgi. "Da kyar ya shawo kanta ta hakura. Yacuro kudi masu yawa ya bata sannan ya koma gida....


®EXTREME HAUSA WRITER'S

NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment