Tuesday, 12 July 2016

MATAR MUTUM 121_125

[5/12,8:30.PM] BY FATIMA

MATAR MUTUM

.
121_125
NA
MRS UMAR


Hameed yana zuwa gida bai sake bata lokaciba, sukayi bankwana da su dady da mom sannan yafito driver ya d'aukeshi airport....

Muhabbat duk ta damu da tafiyar saboda tana tunani kamar in yatafi bazai dawobah, gida tashiga, amma da kaganta kasan tasha kuka, tana shga inna tace, "toh!!! lafiya koh anyi mutuwa ne? " Muhabbat ta girgiza mata kai tace, "a'a Inna dama wai yaya Hameed ne zai k'oma fatako wajen aikinshi shine yazo mukayi sallama. " au dan yakoma wajen aiki shiyasa kike kuka? toh ai sai'ki bishi kitafiwai bama sai andaura aure bah,dama ai ba kanku farauba ai duk soja dan iska ne. "Muhabbat tayi shru tana kallon Inna saboda maganar da take ta fad'i mata tana tsye sai ga Lami ta shgo Inna tace wa Muhabbat maza ta d'auki talla ta tafi haka Muhabbat ta d'auki talla ga ba kwari a jikinta , bayan fitata Inna ta kalli Lami tace, " yar uwa sanu da zuwa dama yanzu nake so naje wajenki. "Toh me yafaru?sha faman. " dama ai tatsoniyar, gizo ai bata wuce ta k'ok'i, wannan dan iskan yaron nan ne wai yau ya koma wajen aikinshi, Lami taso dan Allah kiyiwa boka magana kada yaron nan yasake dawowa cikin garin nan. "Haba mairo sau nawa zanyi maki magana wallahi aiki bokan nan nayi ai ina gaya maki yanda Hameed yabar cikin uwarshi toh haka yabar garin Katsina. " hahaha Lami wai zanga wannan lokacin dama likita yace tana da ciwon zuciya kinga da taji maganar mutuwarshi shkenn itama zata bishi.......

********

Jirgin su Hameed ya isa garin port Harcourt lafiya bayan sun sauka, wayarshi ya dauka ya kira wani yaronshi, soja ne yace yazo yanzu ya d'aukeshi yana airport, ba'a bata lokaciba yazo ya d'aukeshi barrack suka nufa direct yana zuwa ya ajishi k'ofar gidansu, yana kallon k'ofar yaga alamar takalmen kamal kawai sai ya dauri fuska, yana bude k'ofar d'akin kamal na kwance saman kujera 3seaters "Hameed ko ya kalli inda yake kawai ya wuce abinshi, ahankali kamal ya daga kai ya kalli Hameed amma ya kasa yayi masa magana sai kawai yaci gaba da d'anna wayarshi, Hameed bedroom ya nufa ya aje jikarshi sannan ya cire kayan jikinshi ya shga toilet dan watsa ruwa yayi alwala ya tafi masallaci, yana fitowa yaga kamal inda ya sameshi zaune, da sauri kamal ya tashi yace " sanu da zuwa yanzu ka iso kenn but baka kira ni bah. "Hameed ya daga kai ya wurga mashi harara yayi tsk'i yayi fitarsa abinshi , kamal yaji haushi sosai,
Inda Hameed yabar kamal nan ya sameshi da alama koh sallah baibah, Hameed yace " hummm adai tsoron Allah saboda wallahi wannan duniyar bacikinta zamu dauwamabah, kar atashi ai sallah a zauna latsa waya. "Bai tsya yaji amsarshi ba yayi gabah abinshi, lokacin kwanciya yayi kamal yashga bedroom toilet yanufa yayi wanka sannan yafito kayan bacci yasa duk Hameed na kallonshi sai da yagama sannan yanufi gado zai kwanta yana hauwa Hameed ta suri yadauki fillo d'inda ya tada kai ya nufi falo, kamal abin dariya ma yabashi...

Ni kaina sai da nayi dariya nace wannan kamar fad'an mata da Miji.......

®EXTREME HAUSA WRITER'S


NA MRS UMAR

No comments:

Post a Comment